✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu dakatar da Maryam Booth ba-Shugabannin Kannywood

Shugaban kungiyar jaruman Kannywood Alhasa Kwalle ya ce ba za su dauki matakin dakatarwa a kan jaruma Maryam Booth ba a kan bidiyon da ake…

Shugaban kungiyar jaruman Kannywood Alhasa Kwalle ya ce ba za su dauki matakin dakatarwa a kan jaruma Maryam Booth ba a kan bidiyon da ake yadawa.

A tattaunawarsa da Aminiya, Alhasa Kwalle ya ce kasancewar bidiyon ba irin na Maryam Hiyana ba ne, wanda ya sa a lokacin aka dakatar da ita.

Ya yi zargin cewa wanda ya nadi bidiyon ya rika yin amfani da shi domin karban kudade daga jarumar, inda ya bayyana cewa da gangan wanda ake zargin ya yada bidiyon domin ya bata mata suna.

“A matsayinmu na shugabannin wannan masa’antar, nakan yi mamakin yadda mutane suke mana kallo. Abubuwa da dama suna faruwa da suka fi wannan tsanani, amma ba a cika daukansu da zafi ba.

“Abin da ya faru da Maryam kowa ya san cewa da gangan ake so a yi amfani da bidiyon domin a bata masa suna. Ba wai fim ba ne.

“A bidiyonma ta yi kokarin kwace kamarar a lokacin da ta gane ana daukarta, amma ya yi kamar ya goge bidiyon. Amma tun lokacin zuwa yanzu, kusan shekara uku ke nan yana amfani da bidiyon yana karbar kudade wajen ta, kafin daga baya ya saki bidiyon. Na karshe ya kira ne ya ce ta ba shi kudi zai kai maman shi asibiti, inda ta ce ba ta da kudi,”

Ya kara da cewa ana zargin mutum biyu, mace da na miji da sakin bidiyon.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai na Jihar Kano, Malam Ismail Na’abba Afakallah ya ce hukumarsa tana lura da abubuwan da aka shirya domin a sayarwa mutane ne, ba wanda aka yi tozarci da bata suna ba.

Ya ce duk da cewa bai ga bidiyon ba, amma lura da abubuwan da mutane suka fada, ya gamsu cewa ba an dauki bidiyon ba ne a matsayin fim din batsa ko kuma wani abu da zai sa su dauki matakin a kan jarumar.