✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu gurbi a gidan Gwamnatin Gombe a shekarar 2015 — A. A. Abubakar

Wani tsohon dan takarar Majalisar Jihar Gombe daga mazabar Gombe ta Arewa karkashin tsohuwar Jam’iyyar CPC a zaben 2011,, Alhaji Ahmad Adamu Abubakar, ya ce…

Ahmad Adamu AbubakarWani tsohon dan takarar Majalisar Jihar Gombe daga mazabar Gombe ta Arewa karkashin tsohuwar Jam’iyyar CPC a zaben 2011,, Alhaji Ahmad Adamu Abubakar, ya ce babu gurbi don shiga gidan gwamnatin jihar a zaben shekarar 2015, sabod sun gamsu da kwazon Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo.
A. A. Abubakar kamar yadda aka fi saninsa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe inda ya ce samun Gwamna dankwambo alheri ga mutanen Gombe saboda yadda ya game fadin jihar da ayyukan raya kasa, “Wadanda ko mu da muke adawa da shi ya gama da mu,” inji shi.
Ya ce “Duk mai neman takara da dankwambo a shekarar 2015 kan kujerar Gwamna ya hakura sai shekara ta 2019 domin ba kofa ta zama Gwamna. Kuma a shekarar 2019 shi muke so ya kawo mana wanda yake ganin zai iya kamanta irin ayyukan da ya yi mana.”
A. A. Abubakar ya ce duk kasar nan babu jihar da bai sani ba, don haka idan aka lura da hanyoyin da dankwambo yake yi ko mutum hasidin iza hasada ne sai ya yaba masa.
Ya kalubalanci mutanen da suke cewa babu kudi a gari da cewa kudi ba samun mutum suke yi har gida ba, sai ya fita ya nema.