✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wata baraka mai tada hankali a PDP – Barista Jalo

Sabon Sakataren Watsa Labarai na kasa na Jam’iyyar PDP Barista Abdullahi Ibrahim Jalo ya ce babu wata baraka mai tada hankali a tsakanin ’ya’yan jam’iyyarsu…

Barista Abdullahi Ibrahim JaloSabon Sakataren Watsa Labarai na kasa na Jam’iyyar PDP Barista Abdullahi Ibrahim Jalo ya ce babu wata baraka mai tada hankali a tsakanin ’ya’yan jam’iyyarsu ta PDP kamar yadda wasu ke gani.
Barista Abdullahi Jalo, ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu inda ya ce a can baya lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, ya taba hada kai da wasu gwamnoni irin su James Ibori da sauransu suka nemi raba jam’iyyar gida biyu amma daga baya suka ce wai Obasanjo ya je ya same su ya tsuguna ya ba su hakuri an sasanta.
Barista Jalo ya ce waccan rigimar ta fi wannan amma a karshe PDP ta dawo ta hade, “Matsalar kawai ita ce yanzu wasu sun balle suna bayyana damuwarsu kuma ana sauraron su, in Allah Ya yarda za a sasanta saboda Jam’iyyar PDP tana da hanyoyin da take ba ’ya’yanta hakuri a sasanta da wannan rikici ba na sasantawa ba ne da gaba daya ma fita za su yi daga jam’iyyar su koma wata don haka kada gwiwar ’ya’yan jam’iyyarmu ya yi sanyi,” inji shi.