✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar Naira Biliyan 3: Hukumar yaki da rashawa ta ce a dakatar da Sarki Sanusi

Hukumar karbar koke-koken jama’a tare da yaki da yi wa tattalin arzikin jihar ta’annati ta bayar da shawarar a dakatar da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu…

Hukumar karbar koke-koken jama’a tare da yaki da yi wa tattalin arzikin jihar ta’annati ta bayar da shawarar a dakatar da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, sakamakon zargin yin almubazzarnci da kudaden fadar masarautar ta Kano, da ya kai Naira biliyan uku da miliyan 400.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito a yayin da hukumar ke gudanar da bincike ta gano masarautar Kano ta yi almubazzaranci da Naira biliyan uku da miliyan 400 a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017.

A rahoton binciken wanda shugaban hukumar, Muhuyi Magaji, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa binciken ya biyo bayan korafin da hukumar ta samu a kan masarautar Kano.

Hukumar ta yi zargin masarautar ta kashe fiye da Naira biliyan daya da Miliyan 400 kan hanyar da ba ta dace ba, kuma ba ya cikin kasafin masarautar.

Rahoton ya kuma ci gaba da zargin masarautar da kashe fiye da Naira biliyan daya da Miliyan 900 a kan ababuwa na kashin kai da ta ce shi ma ba ya cikin kasafin kudin masarautar.

Hukumar ta ce kashe wadannan kudade ya ci karo da tanadin sashe na 120 na kundin tsarin mulkin  1999 (kamar yadda aka yi was ashen kwaskwarima) da kuma sashe na 8 na dokokin asusun musamman na shekarar 2004. Ta kara da cewa hakan ya kuma saba wa sassa daban-  daban na kundin Final Kod da kuma na hukumar.

Sakamakon haka, hukumar ta ce: “Ja-gaba a wannan zargin badakalar shi ne Muhammadu Sanusi na II da sauran wadanda ake zargi da hannu a ciki, a dakatar da su, har sai an kammala binciken al’amarin.”

Hukumar ta ci gaba da cewa, daukar matakin dakatarwar ya zama wajibi, a matsayin ladabtarwa a harkokin gudanar da mulki, domin hana wadanda ake zargin su yi katsalanda a harkokin binciken.

Hukumar ta kuma ba da shawarar da a kwace kwangilar da aka ba Kamfanin Tri-C Nigeria na sake gina Babban Daki a Kofar Kudu da kuma Gidan Sarki Dorayi.

Har ila yau, hukumar ta kuma ba da shawarar da zarar an kammala binciken al’amarin, to lallai a dauki matakin shari’a kan dukkanin wadanda ake zargi da hannu a ciki.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto masarautar Kano ba ta ce uffan ba game da zarge-zargen da hukumar ke yi mata.

Sai dai wata lauya mai rajin kare hakkin bil adama, Maryam Ibrahim, ta ce wadannan kudaden da ake zance, su ne kudaden da Sarki Sanusi ya gada. Ta ce don haka, ya kamata hukumar ta fara da binciken ko nawa Marigayi Ado Bayero ya bari a asusun masarautar da kuma abin da ya biya a matsayin haraji tare da karin albashin da aka yi wa ma’aikatan fadar.

Ta kuma yi kira da a samu wata hukuma mai zaman kanta ta gudanar da bincike game da zargin almubazzaranci maimakon a ce hukumar da ta ke karkashin gwamnatin jihar.