Search
Subscribe
Bala’in Bobon Bokokon Baragurbi (1)

Bala’in Bobon Bokokon Baragurbi (1)

Kutunguilar kisan kai

Kwaruwa kaskancin kwarai

Turereniyar ture Turai

Jagwalgwalon jijjiga jira-jirai

Matakan mutsuttsukar masai

 

Damuwar darkake Dawai

Rikicin ragargazar rai

Garamba garai-garai

Hatsaniyar haukan kawai

Wayon wuyar wai-wai

 

Lallai-lallai

Jikkatar jikkai

Sha’anin shirirtar Larai

Shan koko bukatar rai

Dirkaniyar rashin dalilai

 

Sakarcin sakaci sarai-sarai

Sunkurun sasarin sukar sakarai

Wautar wawa wasararai

Birgimar bidirin birai

Tsitakar tsikarar tsayayyun tsirrai

 

Caccakar carin cakawaikwaiwa cakwai

Mazarkwaila zakwai

Carkwai

Mazakwai

Dawurwurin dumuiniyar dankwarai

 

Shisshigin shan-kai

Batutuwa bambarakwai

Rai kwakwai

Mutu kwakwai

Baragadar Buwai

 

Dirkaniyar dimuwa

Dagogoragon dadakewa

Dagar dambarwa

Dungun dambacewa

Duga-dugin dogewa

 

Jimamin jimurdar jami’a

Janjamin jan ragamar jama’a

Juyin mako a Juma’a

Jigidar juya akalar sa’a

Jarumai ne masu sana’a

 

Tura ta kai bango

Cucin cutar cocano

Kwaramniyar kwankwadar kokino

Rudani aka hango

Kange-kangen kankane kango

 

Shagalar shagulgulan shagali

Shagirin shedanci

Sharholiyar shashanci

Sharandabar sharbar shan sholi

Shantakewar shan mandular moli

 

Hargagin hautsinewar hankali

Hargagin hali

Tunanin tunkude tubali

Tumbatsar tabarar tabin hankali

Harkallar hasali

 

Turmutsitsin tumbatsar tambabewa

Takun tabarbarewa

Taraliyar tuntsurewa

Takarkarar tabewar tolatsewa

Tawayen tawayar tauyewa

 

Ina dalibai

Masu kisan kai da tabai

Kun nunke kawunanku a baibai

Motsin mutsutsuke matsabbai

Kwakwar kwakume kwabbai

 

Rashi da samu

Kar su sa tumar tumu

Har a kasance an damu

Sasarin sargafewar kamammu

Kai-kawon tunani an gamu

 

Shammatar shaidanu

Shantakewar shiriritar shanu

Soki-burutsun sanin sanannu

Shatale-talen la’anannu

Shakiyancin cin dunu

 

Maganar matsaloli

Tarairayar tsiyataku tsilli-tsilli

Matattarar marasa hankali

Matakan mattatakalar mara hali

Takalar tsokale-tsokalen tsunkuli

 

Fagamniyar fangimar fisge-fisge

Fafutikar fatake

Fifikon falke

Farautar fagage

Fuffukar fiffiken fige-gige

 

Mamakon mokade-mokade

Mirgine-mirgen markade

Kuntukun kade-kade

Rangajin rade-rade

Zogin zabarin zakude-zakude

 

Sha’anin shaye-shaye

Watangaririyar wawaye

Turnukun tawaye

Bilinbituwar bin bala’i baibaye

Magagin mamayar maye

 

Wautar wafce wuyaye

Mugun wasa a kiyaye

A kula da kawaye

’Ya’ya da iyaye

Batun ingarman karfe ba kewaye-kewaye

 

Kwakwar kulle kwayoyi

Jin jiki juyi-juyi

Langabun laulayi

Laga-lagar lallagar layi

Kunkunin kirkirar kaikayi

 

Hattara, hantara

Hankula su tattara

A bar hayaniyar hantara

Natsuwa duk a tara

Sai a samu a sarara

 

Abin da duk a kai rashi

Kar a ce an dau bashi

Ko zare balati mai washi

Hankali duk ya tashi

Rabo ba fushin fashin fashi

 

Ai fafutikar karsashi

Tunanin zuci da rarrashi

A soke matsala da mashi

Ko an jefi tsuntsu ya tashi

Gwafar danko ka kakkabo shi

 

Dungun darussa

Dagar dirasa

Make-maken Makekiyar  madarasa

Mahangar mamular masa

Dawurwurin dumuiniyar dasisa

 

A bar kafa wa kai kusa

Kar a hana bodari yin tusa

Matsaloli su gurgusa

Gantsarar gutsirar gurasa

Fafutika ce dai kar a fasa

 

Jarabar jarabawa

Jajibe-jajiben jibgewa

Jibar jabgawa

Jaye-jayen juyewa

Jam’in jama’ar jami’ar Jamusawa

 

Watangariiyar wulkitawa

Wahalhalun wuntsilawa

Wawurar wuccikewa

Wa-ka-ci-ka-tashin titsiyewa

Wuntsila-gudi-gudin wafcewa

 

Kurmusun kamusun kadamusawa

Kwakume-kwakumen kwakumewa

Kandare-kandaren karajin kumewa

Kadandoniyar kwambon kujewa

Kobarewar kundun kudundunewa

 

Tilascin tilas

Ibilisancin Iblis

Jikkata jiki lilis

Birgimar bugun bulus

Makare maganganu mukus

 

Ana ta kus-kus

Wasu na son cin kuskus

Amma sun gaza katabus

Ballanta su ci gyada tubus-tubus

Masu hali su ci alkubus

 

An dai yi kurmusu kurungus

A tatsuniya an yi algus

Tauna zance kurus-kurus

Jam’in jama’ar jami’ar Jamus

Ragargazar rugumniyar ragas

 

Rummacen rarumar rama rumus

Ambaton algaragis

Hambudar garin budidis

Camamar cin ca’amas

Duddugar dusa dumus

 

ci-da-zuci

ke haifar da kunci

wasu sui ta nukuburci

dare da rana an gaza barci

Ai ta tsiyatakun rashin mutunci

 

Bare-bare

Batancin bangare

Bare-bari ba bare

Bambamin babban Ba’are

Butu-butun babatun bantalar baure

 

Kakarewar karatu

Kwarmaton kurtu

Karkarwar kidan kuntuku

Kwaramniyar kwarakar kwaraku

Kitimurmurar kutu-kutu

 

Sare-sarin surutu

Susucewar sambatu

Sarke-sarken sarautu

Sukurkucewar sullutu

Samamen sunkurun sagaraftu

 

Sunkumemen sunkin sautu

Saisaita sumunin satu

Shasshekar sharubutu

Shakewar shantu

Sigar sauye-sauyen sangartattu

 

Tsawwalar tsadar rayuwa

Tsinin tsikaro tsuwwa

Tsananin tsukukun tsayuwa

Tsilla-tsillar tsomomuwa

Tsallen badaken tsagalgalewa

 

Buga-bugar burka bindiga

Bagun bugi-in-buga

Buhun bahon bagun burga

Bunkasar balagar balaga

Bushe-bushen banga

 

Ladar kwadago

La’adar karin kadago

Lalitar abin sayen karago

Lokacin wuwulawar tsinkayen agogo

Laftun labarai aka kirgo

 

Kwadon mandako

A zubo a koko

A kamfato wa na sako

Mai mura muryarsa na mashako

Tabahuwa ta bulluko

 

Harkar watsatsake

A yi ta keke-da-keke

Alkalami ya zam fekake

Sadarar tafiyar tsutsa a mike

Sai a kauce wa make-make

 

Masu koyi-ka-koyar

Ban da koyi-ka-karkatar

Ko koyi-ka-kayar

Dari-dari yakan haifar

A dinga zaman dar-dar

 

Bala’in bobon bokokon baragurbi

Batutuwa ne babi-babi

Karatun kinkimemen kitabi

Karambanin kalmashe kallabi

Kankambar kinbibi

 

’Yan makaranta kar a shiga dawa

A nemi karuwa

Ban da kwaruwa

Ballantana kassara rayuwa

Lumana tai kawar ban shawa

 

Mu zo mui nazari

Damuwa ce sasari

Sai a sunce asirkar mari

Ilmu shi a babban lamari

Kawar da juhala ba uzuri

 

Dalibai ai guzuri

Ba kwangen cin birbiri

Jajircewar jinkirin jimiri

A  kai ga cikar buri

Da kyautata rayuwar mutan gari

 

A bar siddabarun sihiri

Ko alamta asiri

Balle aikin sirri

A baje komai a sarari

Yin haka ne aiki nagari

 

Juriyar jarumta

Kasurar kin karanta

Masalahar masu makanta

Masu na-mujiya a mutunta

Kowa dai ya fahimta

 

Gangamin gamayya

Tarairayya tarayya

Karajin kuntatar kiyayya

Bi-da-bin bibiyar biyayya

Cikar cabawar cinikayya

 

Laftun liyafa

Kyautayin kyautata manufa

Tafin tafuka a tafa

Albarkacin bakuna a tofa

Maganin matsala a wassafa

 

Ai wa kai masalaha

Tafi ya zam na musafiha

Loto-loto ai ta raha

Dararraku hahaha

Ehe, aha!

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin