Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Bana zan fito da kundin wakoki  biyu – Yahaya Makaho

Mawaqi Yahaya Makaho

Bana zan fito da kundin wakoki  biyu – Yahaya Makaho

Mene ne takaitaccen tarhinka?

Sunana Yahaya Usman wanda aka fi sani da Malam Yahaya Makaho, na kai shekara 12 zuwa 13 ina waka. Abin da ya ja hankalina na shiga harkar waka ba zai wuce neman mafita ba, domin na yi ayyuka daban-daban irin su sayar da kwai da tura baro da sayar da kayan wuta kamar yadda na fada a waka, da na rasa jari sai na zabi in rika waka. Na samu matsalar ido ne tun ina dan shekara uku a duniya. An haife ni a 1982 na samu matsala a 1985 duk abin da na yi da hankalina ina tare da wannan matsala.

Wane kwarin gwiwa ka samu har ya sa ka rungumi sana’a maimakon bara?

Tunda na tashi Allah Ya sa ina kokarin yin wani abu da lafiyayye zai yi. A gidanmu in an je gona yadda kowa zai yi noma haka zan yi ba tare da wani bambanci ba, duk wata gwagwarmaya da ya kamata in koya a yanzu na koya har kiwon shanu na yi tare da yayyena da kanne. Sai na tsinci kaina cikin bara, abin da ya nesanta mu’amalata da su, inda a kowane lokaci ina tunanin yadda zan koma  rayuwa kamar kowa domin sana’ar bara ita ce mafi kaskanci da koma baya fiye da kowace sana’a.

Yaya kake yi wajen rubuta waka?

Yadda marubuta ke tsayawa su kirkiri waka, ni ma haka nake yi. Bambanci kawai suna rubutawa a takarda ni kuma a kwakwalwata. Sanin ka’idojin rubutacciyar waka ban taba zama da wani masanin Harshen Hausa ba, misali wakata ta ‘Hadari’ na yi ta ce kan labarin da wani tsoho ya ba ni kan rayuwarsu ta baya mai cike da taimakon juna da zaman lafiya. Sai ga shi yau wadannan abubuwa sun kau, masu yawan shekaru sun tafi, samari sun yi yawa, gwamnati ba ruwanta.

A mawakan gargajiya kana da wanda kake koyi da salon wakarsa?

Babu. Wakar siyasa na fara yi wadda na yi wa Alhaji Atiku Abubakar. Yau da gobe ce ta hada ni mu’amala da ’yan wasan Hausa, har jaruma Hadiza Gabon ta taimaka min sosai a lokacin da nake gabar son masu sauraren wakokin Hausa su san da ni, ta dauki dawainiyata sosai.

Wace waka ce ka fi shan wahala aikinta?

Wakar da na yi ‘Rayuwar Duniya Iyawa,’ na gina ta ce a kan mahaifiyata ganin irin wahalar da ta sha da ni tun ina ciki har na fito na kuma samu jarrabawar rasa ido, amma ta zame min gata ita da kakannina. Sun yi kokarinsu na nema min magani tun ban sani ba har na sani, sai da na ce a bari haka na hakura. Wata rana na tafi kauye ganin gida na duba, ba kakannina yanzu, wannan tunanin ya sa na kikkiri wakar. Abin da ya sa ta min wahala, dango uku nake yi na hudu ne sauka a waka, amma wannan wakar na yi ta ce dango 19 na 20 ne sauka kuma da kai nake yi.

Wace waka ce ka fi samun alheri?

Duk alherin da nake samu daga Allah ne. Farkon wanda ya fara ban mota a Adamawa yake bai taba ganina ba, ranar da ya gani ranar ya ban mota. Wanda ya yi min dalilin samun gida da jarin buga kundin wakokina guda uku ban taba yi masa waka ba. Haka nake ganin abubuwana suna zuwa daga Allah, wadanda ka yi wa waka daban, alheri inda yake fitowa daban. Misali wannan zuwa ma wanda ya ban mota a Jihar Kebbi ban san shi ba, an ba shi karramawa ya ba ni, shi kuma ya ban kyautar mota.

Masana’antar fina-finan Hausa ta rage karsashi, amma wakoki na bunkasa wane shiri za ku yi martabarku ta dore?

Shirinmu na da wahalar gaske, mutum daya ba zai iya ba kuma ba za a yi kungiyar da za a shawo kan matsalar ba in ba gwamnati ta shigo ba. Sai dai duk abin da mutum zai yi ya sanya Allah gaba, hakan zai sanya ko an daina sauraron wakoki za a rika bibiyar naka don sakonsu. A Jami’ar ABU Zariya wata malama ta fada min ta kammala hada bincikenta a kaina wanda za a shigar da shi dakin karatun jami’a.

Yaya dangantakar mawaka da ’yan kasuwa take?

Dangantaka ce rusasshiya, don yanzu ma harkokin waka sun koma na zamani. Da yawan kasashe sun wuce mu, mu ne aka bari a baya wurin ’yan kasuwa su sayar da hajarmu sai sun ga dama su biya mu. A bana ina shirin fito da kundi biyu na wakokina, dayan yabon Annabi ne wakoki takwas dayan kuma wakoki ne na fadakarwa su ma takwas ne.