✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun inganta wutar lantarki

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da ginin cibiyar wutar lantarki mai karfin megawatt 700 a garin Zungeru da ke Jihar Neja.…

A makon jiya ne Shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da ginin cibiyar wutar lantarki mai karfin megawatt 700 a garin Zungeru da ke Jihar Neja. Wannan cibiyar za ta zama ta hudu bayan cibiyar wuta da ke Kainji da Jebba da kuma Shiroro, wanda kuma an kirikiro gina cibiyar ta Zungeru ne duk a cikin shirin gwamnatin tarayya na ceto matsalar wutar lantarki a Najeriya. An yi kiyasin za a kashe Naira biliyan 162.9 cikin shekara 4 wurin gina cibiyar wutar lantarki ta Zungeru, kuma bankin EdIM da ke China da kuma gwamnatin Najeriya suka yi hadin gwiwa wurin gina cibiyar, inda bankin zai bayar da kashi 75; Gwamnatin tarayya kuma za ta ba da kashi 25, sai dai banki zai bayar da bashin kudin ne inda kuma za a biya shi bisa sharadin dogon lokaci. Ministan Wutar Lantarki Farfesa Chinedu Nebo ya ce tuni Hukumar NEC ta amince a cire Dala biliyan 1.72 don gina cibiyar, wanda kuma a yanzu har an cire kudin (kashi 25).
Bayanan da aka gabatar a lokacin kulla yarjejeniyar sun ba da kwarin gwiwa cewa a yanzu gwamnati da gaske take don ta shawo kan matsalar wutar lantarki, inda masu sharhi suka ce an fara taka tsanin shawon kan matsalar wutar lantarki.
Shekara 32 suka gabata aka fara batun gina cibiyar wutar lantarki a Zungeru, amma aka rika samun tsaiko, sai a wannan karon ne aka kammala dukkan shirye-shiryen da ake bukata. Kodayake a yanzu za a iya cewa kwalliya za ta iya biyan kudin sabulu tun da bankin EdIM yakan jajirce wurin cim ma duk wani kuduri da ya sanya a gaba dangane da al’muran da suka shafi Afrika.
Shekaru da dama da suka wuce ‘yan siyasa sun sha kaddamar da harsashin ayyukan raya kasa, amma kuma a karshe sai a yi watsi da su bayan makudan kudade da aka ware don wadannan ayyukan, inda kuma aka nemi kudaden wadannan ayyuka sama ko kasa aka rasa. Gina cibiyar wuta ta Zungeru ta fuskanci irin hakan.
A yanzu wannan dama ce da ya kamata gwamnati ta karya alkadarin kasa samar da wutar lantarki mai karfin megawatt dubu 6 da ta yi. Musamman ma da yake akwai tsaunin Mambila da kuma dam din Gurara da ke Suleja a Jihar Neja.  Babu wani dalili da za a ce aikin ya samu matsala tun da har Minista Nebo ya bayyana tuni aka cire kashi 25 na kudin da za a yi aikin. Idan har shirye-shiryen gwamnatin tarayya na shawo matsalar wutar lantarki suka samu nasara tattali arzikin Najeriya zai bunkasa, kuma za a samu wadansu hanyoyin za a rika gudanar da kasuwanci da sana’o’i ba tare da wahalhalu ba, tun da kowa na da masaniyar rashin wutar lantarki na daga cikin manyan matsalolin da suka hana al’amura rawar gaban hantsi a Najeriya.
kasar Afrika ta Kudu tuni ta samar da wutar lantarkin da take bukata, kuma sun samu hakan ne ta hanyoyin da dama ba kamar yadda Najeriya ta dogara a kan hanya daya ba kawai.  Don haka ya kamata Najeriya ta samar da wadansu hanyoyi ba wai kawai hanyar amfani da ruwa ko dam wurin samar da wuta ba.  A duba fa Afrika ta Kudu tana da wutar lantarki mai karfin megawatt dubu 40 kuma tana da yawan mutane miliyan 50.  Najeriya mai yawan mutane fiye da miliyan 150 ta bugi kirjin ta samar da wutar lantarki mai karfin megawat dubu 6, wanda a yanzu al’amarin ke hawa da sauka daga megawat 3500 zuwa dubu 4.
Dukkan cibiyoyin ba da wutar lantarki na Najeria suna Jihar Neja ne, kuma tuni majalisa ta sa hannu kan kudurin Bunkasa Yankunan da ke Samar da Wutar Lantarki (HYPADEC) kusan shekara goma da suka gabata.
Abin mamakin shi ne, ko a lokacin da Shugaba Jonathan yake jawabi yayin kaddamar da cibiyar wuta ta Zungeru ya ce bai san da wannan dokar ba, ya kuma nemi a mika masa ita don ya duba ta. Hukumar HYPADEC za ta rika kawo matakan da za a rika shawo kan matsalolin da suke fuskantar yankunan da suke samar da wutar lantarki wadanda suka hada da Kogi da Kwara da kuma Neja.
Idan har ana so a samu nasarar gina cibiyar wuta ta Zungeru, to ya kamata ma’aikatar wuta da kuma ta ruwa su tabbatar masu kwangilar sun dauki ‘yan Najeriya aiki, musamman ma ‘yan asalin yankin da ke samar da tashar wutar. Ta haka ne ‘yan yankin za su tabbatar da an ba su mahimmanci kuma za su taimaka wurin ganin ta dore.