✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Mutum 400 sun yi gudun hijira zuwa Sakkwato

Bayan shafe shekara 60 suna zaune a Kondiga da ke Jihar Borno wasu ’yan asalin Jihar Sakkwato mazauna garin sun yiwo gudun hijira sakamakon hare-haren…

Bayan shafe shekara 60 suna zaune a Kondiga da ke Jihar Borno wasu ’yan asalin Jihar Sakkwato mazauna garin sun yiwo gudun hijira sakamakon hare-haren da ake zargin ’yan Boko Haram da kaiwa ba kakkautawa.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci kauyen Maikujera a karamar Hukumar Rabah inda mutum 400 suka yiwo gudun hijirar ta iske kananan yaran da aka yiwo hijirar da su cikin firgici ta yadda da zarar suka ga bakuwar fuska sai su sheka da gudu bisa zaton ’yan Boko haram ne suka je.
Alhaji Usman mai shekara 60 wanda ya ce tun yana da shekara biyar ya bar Sakkwato zuwa Borno tare da mahaifinsu ya ce sun yanke shawarar dawowa Sakkwato ne kafin lamarin ya lafa, “A shekaranjiya ne (Talatar makon jiya) bayan Sallar La’asar muna cikin masallaci kawai muka ji karar bindiga da abubuwa masu fashewa, sai muka yi daji muka haye itatuwa can muka kwana har safe ba ruwa ba abinci. Da safiya muka isa kauyen Rijiyar Fulani muka yi Sallah sa’anna muka shigo Kondiga muka samu wasu na kashe wuta a gidajensu, mu da namu suka kone muka yanke shawarar mu kwaso sauran iyalanmu da suka rage zuwa garinmu na asali,” inji shi.
Ya ce mayakan da ake zargin ’yan Boko Haram ne komai suka gani in mai kyau ne sukan tafi da shi in bai da kyau su kone shi, “Abin takaici in sun ga mace mai kyau ko namiji matashi sai su tafi da su suna cewa ‘mu je ku yi aikin Allah.’ A gaskiya da jami’an tsaro suna yin aikinsu yadda ya kamata da wadannan mutane ba su fi karfinmu ba har su iya kona mana gari gaba daya,” inji shi.
Shi kuwa Malam Muhammad Tarifa wanda manomi ne kuma masunci ya ce da suka ji karar harbi sai suka sheka daji ba su dawo ba sai 12:00 dare, inda suka iske an kone komai nasu. “Na kwashe shekara 45 a Borno bayan na bar Sakkwato kuma ko yanzu kura ta lafa za mu koma can da zama. Mutanen da ke harbinmu da idona na gansu da kayan soja kuma motarsu fenti soja ke gare ta, bambancinsu da zarar sun zo za su rika harbi ne sabanin soja,” inji shi.
Ya ce sauran mutane suna zuwa, kuma sun samu tarbar da ta dace daga karamar Hukumar Rabah wadda ta bayar buhun shinkafa 10 da na gero 10 da Naira 5000 na cefane ga kowane magidanci.
Abdullahi Yahaya Magajin Maikujera wanda shi ne Hakimin garin ya tabbatar wa Aminiya cewa mutanen ’yan asalin garin ne kaka da kakanni kuma za su ci gaba da taimaka musu. Ya cesun zo ne a mota Daf yara da mata sun yi baki saboda wahala da yunwa.
Ya ce kusan dukan mazan a waje suke kwana ba gida ko dakin da za a ajiye su, matan kuma na gidan ’yan uwa inda ake taimaka musu, sai ya roki gwamnati ta taimaka musu da gidaje da abinci da tufafi.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Zayyanu Gandi ya shaida wa wakilinmu cewa sun taimaka wa jama’ar da filaye da abinci da tufafi da Naira 5000 ga kowane magidanci, kuma za su sake duba abin da za a yi ga mutanen.