Da Dumi Dumi

Buhari ya nada tsohon ministansa ya gaji Abba Kyari

Sabon Shugaban Ma'aikata a Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon ministansa na harkokin waje, Farfesa Ibrahim Gambari, a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya tabbatar da nadin ana daf da fara taron Majalisar Ministoci a Fadar Shugaban Kasa.

Farfesa Gambari, wanda ya rike mukamin Ministan Harkokin Waje lokacin da Buhari ke mulkin soji, zai gaji Malam Abba Kyari, wanda Allah Ya yi wa rasuwa bayan ya yi fama da COVID-19 a watan jiya.

Sabon shugaban ma’aikatan ya taka muhimmiyar rawa wajen kwantar da kurar da ta taso bayan yunkurin da aka yin a dawo da tsohon Ministan Sufuri a Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Umaru Dikko.

A wancan lokacin Farfesa Gambari na cikin mutanen da ke da kusanci da shugaban kasar.

ADVERTISEMENT

Tsohon malamin jami’ar ya kuma rike mukamin Wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya