Da Dumi Dumi

Buhari ya nemi gwamnonin APC su ba shirin yaki da cin hanci goyon baya

Daga hagu Mista Boss Mustapha da Gwamna Lalong na Filato da Shugaban APC na Qasa Adams Oshiomhole a wajen taron
Daga hagu Mista Boss Mustapha da Gwamna Lalong na Filato da Shugaban APC na Qasa Adams Oshiomhole a wajen taron

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin Jam’iyyar APC su ba shirin Gwamnatin Tarayya na yaki da cin hanci da rashawa goyon baya a jihohinsu. Shugaban Kasar ya bayyana haka ne, lokacin da yake jawabi a wajen taron gwamnonin Jam’iyyar APC 20 da aka gudanar a Jos a ranar Litinin da ta gabata.

Ya ce “Ina kira ga gwamnonin APC ku kara zage dantse wajen bai wa wannan shiri na yaki da cin hanci goyon baya a jihohinku, domin ganin an magance wannan matsala, saboda hadarin da ke tattare da ta.”

Ya ce “Muna son mu gina al’umma ce wadda za ta rika amfani da dukiyar kasa, wajen yi wa al’umma aiki baki daya.”

Shugaban wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Boss Mustapha ya wakilta, ya yaba wa taron kan yadda ya mayar da hankali kan bunkasa sufuri da kiwon lafiya da ilimi da agaza wa al’umma a jihohi.

Ya ce tuni Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali kan wadannan abubuwa, inda ta kashe makudan kudi a bangaren gina titin jiragen kasa da gina hanyoyin mota.

ADVERTISEMENT

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi kokari wajen samar da tsaro a kasar nan, don ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Kuma ta samu gagarumar nasara, don haka ya yi kira ga al’ummar Najeriya su ci gaba da hada hannu da gwamnati, don ganin an samu ci gaban da ake bukata.

Sai Shugaba Buhari ya yi kira ga gwamnonin su kara mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan kyautata rayuwar al’umma a jihohinsu.

Da yake jawabi, Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa Kwamared Adam Oshiomhole, kira ya yi ga gwamnoni kan su ci gaba da yin aiki da ka’idojin Jam’iyyar APC.

Ya ce idan aka ci gaba da yin haka za a yi abubuwan da za su kyautata rayuwar al’ummar kasar nan.

Kwamared Adam Oshiomhole ya yaba da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na rufe kan iyakokin kasar nan.  Ya ce wannan mataki ya yi dai dai, don haka ya yi kira ga al’ummar Najeriya su bai wa gwamnati goyon bayan kan wannan al’amari.

“Ba za a bude kan iyakokin nan ba, har sai kasashen da muke makowabtaka da su, sun mutunta dokokinmu ta hanyar daina shigo mana da kayayyaki ta barauniyar hanya,” inji shi..

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya