✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in ga mata sun rungumi harkar noma – Hajiya Kulu Abdullahi

Hajiya Kulu Abdullahi ita ce babbar ’yar shahararren manomin nan marigayi  Ali Namani Kotoko, kuma ita ce Mataimakiyar Magatakardar Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke…

Hajiya Kulu Abdullahi ita ce babbar ’yar shahararren manomin nan marigayi  Ali Namani Kotoko, kuma ita ce Mataimakiyar Magatakardar Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato. A zantawarta da Aminiya ta tabo tarihinta da nasarori da kalubalen da ta fuskanta a rayuwa:

 

Tarihina:

Sunana Hajiya Kulu Abdullahi.   An haife ni a ranar 24 ga watan Afrilun 1963 a garin Wasagu.  Maifina marigayi Ali Namani Kotoko sanannen manomi ne a kasar nan. Ni ce ta fari a cikin ’ya’yan mahaifinmu. A lokacin muna yara ba a san kabilanci ba irin wanda ake yi  yanzu, abin da ya sanya aka  kai ni yaye wurin wata Bayarbiya aminiyar mahaifanmu wadda Allah bai ba ta haihuwa ba, ta nemi izini ga mahaifana za ta je da ni garinsu na Ogbomosho. Allah Ya yi mata rasuwa ne a wani gari da ake kira Bade a can Ogbomoso a wani hadarin mota da ya rutsa da mu.  Hakan ta sa aka mayar da ni gida wajen iyayena, amma a lokacin ko Hausa ba na ji. A haka aminin mahaifina ya ce a sanya ni a makarantar boko don in na yi hulda da yara ’yan uwana zan iya yin Hausa.  Na yi karatun firamare daga nan na shiga Kwalejin ’Yan mata  a 1975 a garin Tungar Magajiya na kammala bayan shekara biyar don a lokacin su ake yi. Na yi digiri a Jami’ar Usman Dan Fodiyo a fannin tarihi. Na yi aure da Malam Audu Zuru a yanzu Farfesa ne kuma shi ne Shugaban Jami’ar Usman Dan Fodiyo a yanzu. Na samu aikin gwamnati tun ina hidimar kasa a lokacin aiki ba ya wuya. Na fara da karantarwa a 1986, bayan dawowa daga kasashen waje ni da maigidana na koma Kamfanin Sadarwa na Kasa (NITEL)  da aiki. Da na yi shekara shida a wurin sai na koma Jami’ar Dan Fodiyo da aiki inda a yanzu na zama Mataimakiyar Magatakardar Jami’ar.

 

Kalubalen da na fuskanta:

Kalubalen suna da yawan gaske.  Na farko yanayin rayuwa a matsayina na ma’aikaciya za ka ga abin da kake samu ba zai ishe ka har ka taimaki wadansu ba.  Ga tarnaki a wajen gudanar da lamuranka. Zamana na mace ma ya sanya na samu kalubale a yanayinmu na addini da al’ada. Musulunci ya shata yadda mace za ta yi hulda amma al’ada tana hana mace cimma burinta don ni kaina al’adar ta hana ni don karatun shari’a na so yi. Noma da nake sha’awa, in mace ta ce za ta yi sai a rika yi mata wani irin kallo, ka ga wannan ma wani kalubale ne.

 

Burina a rayuwa ya cika:

Alhamdulillah, rayuwa yadda ya kamata mutum ya dauke ta tun ran gini tun ran zane.   Duk wani abu da mutum zai gudanar iyarwa ne kawai. Ni dai gaskiya tarbiyyar da na samu wajen iyayena ita ce sadaukarwa da jajircewa wadannan  ne suka taimaka min wajen cika burina. Duk abin da na sanya a rayuwata Allah na taimaka min ina samun sa kuma na kan nemi abu a kan ka’ida, don haka ba na manta cewa ni matar aure ce.

 

Abin da nake son a tuna ni da shi:

Abin da nake son mutane su tunani da shi bai wuce mutane su sani na yarda ni mace ce da Allah Ya halitta wadda ta yi hulda bisa yadda addini ya aminta. Ina kokarin kwatanta karantarwar addini a huldata da jama’a.  Koyaushe tunanina al’umma su samu ci gaba. Arzikin duniya ba kudi ba ne, canja rayuwar wani shi ne arziki, saboda gobensa ta yi kyau. Kuma ina son ’yan gidanmu su tuna da ni kan yadda na jagorance su a matsayina na babba a dorewar hadin kan da muka samu bayan wucewar mahaifinmu, ban bari zumuncinmu ya yi sako-sako ba, wannan dagewar ma ina son a rika tunani da ita.

 

Tarbiyyar ’yan mata a yanzu:

Tarbiyarsu akwai matsala abin bakin ciki kuma laifinmu ne iyaye. Fiye da kashi casa’in na tarbiyyar da iyayenmu suka ba mu, ba ita ce muke bai wa ’ya’yanmu ba, wannan bayarwar da muka yi ita ce matsala. Kowa ya san in tarbiytar mata ta lalace, al’umma ta shiga garari, don tarbiyya a hannun mace take saboda kasancewarta uwa.

 

Shawara ga mata:

Mata mu canja lamarinmu, abin duniya da muka sanya gaba ba shi ne makoma ba, duk matsalolin da suka gitta a cikinmu saboda abin duniya ne. Ba wanda zai ce ba ya da amfani don ba wanda zai ce ba ya son kudi amma hanyar da aka samu kudin ce ya kamata a duba.

Sannan a wurin neman ilimi a gane ba iya rubutu da karatu ba ne kawai, tarbiyya na da matukar muhimmanci ita ce za ta dora yaranmu a kan tafarki madaidaici, su san daidai da rashin daidai. Uwar da ke shaye-shaye ba za ta hana yaranta su yi ba.   Wacce ke zuwa wurin shagali da yin kwaliyar zamani ita ma ba za ta hana ’ya’yanta yi ba. Iyaye mata sun lalace, shawarata a nan ita ce mu koma ga Ubangiji da kyakkyawan tarbiyyar da iyayenmu suka bar mana.

Kuma ina son mata su gane sana’ar noma ba ta maza kadai ce ba.  In dai mace za ta iya zuwa kasuwa da wurin biki ban ga dalilin da zai sa ba za ta iya zuwa gona ba. Sana’ar noma harka ce mai albarka fiye da yadda ake zato.  Ba dole sai mace ta zauna a gona ba, ina bai wa mata shawara su koma gona shi zai sanya yaranmu su yi koyi da mu musamman a bangaren noma.

 

Sha’awata ga harkar noma:

Da muka fita kasar waje da mijina na

dakatar da noma bayan mun dawo daga Turai sai na gaya wa mahaifina ina son in koma noman. Sai ya ce mini Kulu noma ba naki ba ne lokacin ban fahimce shi ba sai daga baya don gwamnati ba ta taimaka wa manoma, don haka ba su da kwarin guiwa. Za ka ga manomi ya yi noma amma ba riba sai asara. Ba a bai wa bangaren muhimmanci ba. Komai kai za ka samo abinka, dole ka samo shi cikin tsada, sannan idan ka tashi sayarwa, ka sayar asara. Na kasashen waje ya fi naka arha da tsabta da kyau don sun fi gyarawa.  A lokacin da na dawo noman mahaifina ba ya da lafiya, bayan ya rasu a shekarar 2014 sai muka debe amfanin gonar da muka shuka noman ya zame mana asara. Da wata shekara ta zagayo kannena suka ce mu bar noman, na ce ba zai yiwu ba sunan da mahaifinmu ya yi cikin noma da yadda yake son sa cikin zuciyarsa kuma ya fada mana ko bayan ransa mu rike noma a matsayin sana’a. Da muka ci gaba ne muka yi sa’a gwamnati ta juyo kan harkar sai na tabbata noma sana’a ne duk abin da za ka yi ka ci riba ba kamarsa.   Na ci gaba da noma ne don ina son kada sunan mahaifina ya mutu a manta da shi kuma na rike ne don sabo da shi, bayan kasuwanci.

 

Sirrin shaharata a noma

Kada ka manta mahaifina shahararren manomi ne na fara taka sawunsa, kafin in cim masa akwai aiki don muna da bambanci da shi. Ya yi noma ne saboda suna, mu ko muna yi ne saboda riba, dole ne mu kula da wasu abubuwan da dama, akwai aiki. A maganar shahara kuwa a gaskiya ina ganin abin da ya burge mutane a sharata a Kebbi bai fi zamana mace ba, na tabbata akwai manoma da ban taka kafarsu ba, amma dai suna mamakin yadda mace ke noman da nake yi.  A bara da na samu buhun masara da dawa 259 a wata gona kuma 522 a wata, ban samu shinkafa ba domin buhu 15 Kawai na yi, sabanin 32 da na samu a wata shekara.  Gona kuma ina noma mai hekta 18 da mai 102 da na gada a wurin mahaifina da fadama mai hekta 52.  A duk sa’ar da za mu fara aikin gona bayan masu gadi mukan dauki mutum 50 don shuka, noma da sanya taki a sabon salon da muke amfani da shi.   Mutum ashirin zuwa da biyar sukan yi fiye da kwana 10 suna aiki, haka a girbi.  Harkar tana da kalubale saboda ba mu da injuna irin na zamani, da tasirin ya fi haka.

 

Yunkurin karfafa wa mata gwiwa su rungumi noma

Abin da nake fatan gani maza da hukuma su bai wa mata goyon baya a taimaka musu da abin hannu na tallafi in an cire amfanin gona sai a biya da shi ko a raba riba. Ina da shirin da zan fito da shi da kudina don taimaka wa mata su yi noma a san su ma suna iyawa. Ya kamata gwamnati ta yi yekuwar mata su yi noma don addini ya bai wa mata damar su yi sana’a sai kuma a ba su kwarin gwiwa da kula, don ita ce na samu mahaifinmu ya bar mana baiwar kasa da tarbiyya shi ya sa wadansu ke ganin har yanzu mahaifinmu Namani bai mutu ba.

Iyali

Allah Ya albarka ce ni da ’ya’ya hudu maza biyu mata biyu, matan su duka likitoci ne namiji daya ke sakandare, dayan kuwa ya rasu.