✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Catherine Ashton ta Tarayyar Turai ta gana da Mursi

Catherine Ashton, Babbar Jami’ar difulomasiyar Tarayyar Turai ta EU, ta bayyana cewa ta ziyarci hambararren shugaban kasar Masar, Muhammad Mursi don ta tabbatar wa iyalansa…

Shugaba Mursi a lokacin d ayake ganawa da Catherine Ashton.Catherine Ashton, Babbar Jami’ar difulomasiyar Tarayyar Turai ta EU, ta bayyana cewa ta ziyarci hambararren shugaban kasar Masar, Muhammad Mursi don ta tabbatar wa iyalansa cewa yana nan lafiya, kuma yana samun ganin talabijin. Kuma ana sanar da shi halin da kasa take ciki.
Sai dai kafafen yada labarai sun yi hasashen cewa Misis Ashton tana nema wa Shugaba Mursi mafita, idan har ya amince ya hakura da shugabancin kasar. Ta dai karyata wannan labarai da ake yadawa. “A ganawar da muka yi ta tsawon sa’o’i biyu, na bayyana masa cewa ba zan wakilce shi ba, domin idan na yi kuskure ba zai iya yi mini gyara ba,” injita.
Wannan ziyara da Ashton ta kawo sharadi ne da ta gindaya na ganawa da shugabannin da suka kawar da Mursi. “Na sanar da su ba zan zo ba, matukar ba za a bar ni in gana da shi (Murshi) ba,” inji Ashton.
An tsare Shugaba Mursi, an kuma hana kowa ya gana da shi, tun bayan da aka hambarar da gwamnatinsa, a ranar 3 ga Yulin bana. Hukumomin Masar sun ce ana tuhumarsa ne da aikat alaifukan d asuka hada da kisan kai, a lokacin da ya tsere daga kurkuku cbikin shekarar 2011, inda aka tsare shi lokacin da aka yi zanga-zangar da ta hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak.
Ms Ashton, wadda babbar jami’ar difulomasiyya ce a Turai, tana ta kai kawo tsakanin masu mulkin Masar da kungiyar ’Yan uwa Musulmi, a kokarinta na shawo kan yawan zubar da jinin da ake yi a kasar. Kuma ita kadai ce jami’ar da aka amince da ita wajen yin sasanci a tsakanin bangarorin da ke fada da juna.
Masu mulkin Masar sun kyale jakadiyyar Tarayyar Turai, Catherine Ashton ta gana da hambararren Shugaban kasar, Muhammad Mursi, tun bayan sojojin kasar suka daure shi trsawon wata guda da ya gabata.
Babbar Jami’ar Harkokin Wajen Tarayyar Turai ta EU, Catherine Ashton, ta yi tattaunawar sa’o’i biyu tare da Mursi, a ranar Litinin din da ta gabata, kamar yadda Mai Magana da yawunta, Maja Kocijancic ya bayyana a shafin sadarwarsa na Twitter.