✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea na zawarcin Zidane

Rahotanni na nuna cewa kungiyar Chelsea ta fara yunkurin yin waje da mai horar da ’yan wasanta Maurizio Sarri bisa la’akar da yadda kungiyar ke…

Rahotanni na nuna cewa kungiyar Chelsea ta fara yunkurin yin waje da mai horar da ’yan wasanta Maurizio Sarri bisa la’akar da yadda kungiyar ke kwan-gaba-kwan-baya.

An rawaito cewa kungiyar na zawarcin tsohon kocin Real Madrid, Zinedine Zidane, wanda yanzu haka yake zaune ba tare da kulob ba bayan ya yi murabus daga horar da ’yan wasan  Real Madrid a kakar bara, kwanakin kadan bayan sun lashe gasar Zakarun Turai karo na uku a jere.

Chelsea na zawarcin Zinedine Zidane ne da zimmar ya dawo da martabar kungiyar, bisa la’akari da yadda ya horar da Real Madrid suka zame wa kowa ciwon ido a duniyar kwallon kafa.

Jaridar The Sun ta rawaito cewa Majalisar Koli ta kulob din Chelsea na tunanin dauko Zinedine Zidane sannan ta biya shi albashi mafi tsoka a tsakanin masu horar da ’yan wasa.

Kamar yadda ake cewa zamani goma sarki goma, kowane mai horar da ’yan wasa yakan ya zo da irin nasa salon, da kuma irin ’yan wasan da yake so.

Misali a kakannin wasu biyu da suka gabata, tsohon dan wasan Najeriya Bictor Moses yana cikin manyan ’yan wasan kungiyar Chelsea saboda irin salon wasa da tsarin Antonio Conte, amma bayan tafiyarsa, shi ke nan shi ma Moses ya zama dan zaman benci, wanda hakan ya sa dole ya tafi kungiyar Fenerbahce a matsayin aro.

Masu sharhi a kan kwallon kafa suna ganin idan Zinedine Zidane ya karbi ragamar horar da kungiyar Chelsea, Bictor Moses zai samu damar ci gaba da wasa a kungiyar.