Cikakkun sunayen Hadiman Osinbajo 35 da Buhari ya kora

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kori hadiman mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo su 35 daga yin aiki a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa Abuja.

Majiyarmu ta samu cikakkun sunayen hadiman wadanda mafi yawa daga cikinsu na hannun daman Osinbajo ne.

Daga cikin jerin sunayen wadanda lamarin ya shafa sun hada da Ajibola Ajayi, ‘yar tsohon gwamnan jihar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi maitaimakawa Shugaban kasa (a ofishin mataimakin shugaban kasa) a fannin Shari’a. Ta kasance tsohuwar  Maiba shugaban Kasa shawara ta musamman daga watan Oktoba 2015 zuwa Mayu 2019.

A jerin sunayen akwai Lanre Osinbona, Babban Mataimaki na Musamman (SSA) a kan lamarin Fasahar Sadarwa ICT; Imeh Okon, SSA akan Lantarki; Jide Awolowo, Mai bada shawara ta Musamman akan Man Fetur da Iskar Gas; Gambo Manzo, mai bada shawara kan lamarin Siyasa da Edobor Iyamu, mai bada shawara na musamman SSA kan bangaren lamuran yankin Niger Delta.

Sauran sunayen sun hada da:

ADVERTISEMENT

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya