✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An killace ‘yar Buhari bayan ta dawo daga Birtaniya

Daya daga cikin ’ya’yan Shugaba Muhammadu Buhari ta killace kanta bayan dawowarta daga Birtaniya, daya daga cikin kasashen da cutar Coronavirus ke karakaina. Uwargidan shugaban…

Daya daga cikin ’ya’yan Shugaba Muhammadu Buhari ta killace kanta bayan dawowarta daga Birtaniya, daya daga cikin kasashen da cutar Coronavirus ke karakaina.

Uwargidan shugaban kasar Aisha ce ta bayyana hakan a wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter.

“Bisa shawarar mai girma ministan lafiya, da Kwamitin Cika-aikin Shugaban Kasa a Kan COVID-19, da kuma Hukumar Yaki da Cututtuka Maus Yaduwa ta Najeriya, ta killace kanta duk da cewa ba ta nuna wasu alamu cewa tana dauke da cutar COVID-19 ba”, inji Hajiya Aisha Buhari.

Sai dai kuma uwargidan shugaban kasar ba ta fadi ko wacce ce daga cikin ’ya’yan nata ta killace kanta ba.

Hajiya Aisha ta kuma ce ta rufe ofishinta har tsawon mako biyu.

“Yayin da wadanda aikinsu ya zama wajibi za su yi aiki daga gida, [an dauki wannan mataki ne] saboda wasu ma’aikatan da ba su jima ba da dawowa daga Birtaniya.”

Ranar Laraba ne dai hukumomin Najeriya suka bayar da sanarwar dakatar da matafiya shigowa daga wasu kasashe 13, ciki har da Birtaniya.

Sauran kasashen sun hada da Amurka, da China, da Switzerland, da Iran, da Holand, da kuma Italiya.

Sai kuma Japan, da Koriya ta Kudu, da Spaniya, da Faransa, da kuma Jamus.

Wannan hanin dai zai fara aiki ne ranar 21 ga watan Maris, lamarin da ya sa wasu ’yan Najeriya shagube cewa ashe akwai dalili.