Da Dumi Dumi

Coronavirus: Sakamakon Ali Nuhu, Maishadda da sauransu ya fito

Biyo bayan gwajin da aka yi Ali Nuhu, furodusa Abubakar Bashir Maishadda da darakta Hassan Giggs da mawaki Ado Gwanjam sakamako ya nuna cewa dukansu ba sa dauke da cutar ta coronavirus.

Aminiya ta ruwaito cewa za a gwaja su ne bayan wani taro da suka halarta na karrama ’yan fim, inda ake zaton akwai wani wanda yake dauke da cutar.

Maishadda ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “kowa zai iya kiran kansa masoyi, amma sai an shiga tsanani ake gane masoyi na hakika. Muna godiya da dukkanin addu’a, kuma muna cikin koshin lafiya masoya. Allah Ya bar kauna.”

Da yake yi wa Aminiya bayanin kan sakamkon, furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya ce, “dama ba mu da ita. Kuma sakamakon ya nuna cewa ba mu da ita. Taro muka na mutane da yawan gaske, sai ake tunanin a cikin taron akwai mai ita, kuma shi ma ya fito ya karyata batun yana da ita.”

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya