✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da gyaran lasifika nake gudanar da rayuwata – Dan Yaro

Malam Auwal Usman Goni wanda ake kira da  danyaro ya ce gyaran lasifika ta yi masa komai a rayuwa domin da wannan sana’a yake gudanar…

Malam Auwal Usman Goni wanda ake kira da  danyaro ya ce gyaran lasifika ta yi masa komai a rayuwa domin da wannan sana’a yake gudanar da duk wata hidimar rayuwar iyalansa.

Malam danyaro wanda kuma shi ne Shugaban Masu Mata daidaya na Jihar Gombe ya ce yana wannan sana’a ta gyara lasifika da talabijin ne fiye da shekara 27 wanda ya koya wajen mai gidansu da ake kira Oga Peter.

A cewar danyaro, tunda ya fara koyon wannan sana’a ta gyara bai taba dainawa  ya koma wata ba har zuwa yanzu.

Ya ce ya fi mayar da hankali ne wajen gyaran lasifika ne tunda mai gidansu ya bar Gombe amma a lokacin da yake nan ya fi gyara talabijin.

Kamar yadda ya koya shi ma ya koya wa wadansu da dama wannan sana’ar inda yanzu suka zama magidanta masu cin gashin kansu.

“Da sana’ar nan duk wata matsala ta rayuwa ina iya biya wa kaina ba tare da dogara da abin hannun abokai ko na ’yan uwa ba,” inji danyaro.

Auwal Usman Goni, ya yi kira ga gwamnati cewa ta kula da masu sana’o’in hannu domin tallafa musu.

Ya ce lokaci ya yi da kowane mutum zai nemi sana’a domin an wuce lokacin zaman banza.