✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun Kasuwanci: Kasafta Ribar Kasuwanci (3)

A wannan makon zan ci gaba da wannan makala ta Kasafta Ribar Kasuwanci da na fara makonni biyu da su ka gabata. A makon farko…

A wannan makon zan ci gaba da wannan makala ta Kasafta Ribar Kasuwanci da na fara makonni biyu da su ka gabata. A makon farko na fara bayanin yadda dan kasuwa zai kasafta ribar da ya samu daga harkarsa ta kasuwa a matsayin dabarar kasuwanci, inda na yi nuni ga dan kasuwa cewa babbar dabara ce gare shi  da ya ware wani kaso na ribar da ya samu domin kara karfin jarinsa. Na kuma shawarci dan kasuwa da ya ware wani kaso daga ribarsa domin inganta ko sabunta ko musaya injuna da motocin da ya ke amfani da su wajen tafiyar da harkarsa;   na kuma yi gargadi da jan hankali a makalar cewa ware kudi daga cikin ribar kasuwanci domin sabunta ko musaya motoci da injina da sauran kayayyakin tafiyar da harka ya zama dole domin a kullum karfinsu karewa ya ke yi yayin da ake amfani da su wajen tafiyar da harkar. Na kuma nuna  mahimmancin wannan al’amari, domin bukatar sabunta wadannan kayan aiki na iya samun dan kasuwa a lokacin da bai shirya ba, ya kuma saka shi a wani mawuyacin hali, yayin da wadannan ababen aiki suka kasa ba shi sukunin sayen wasu.
A makon da ya gabata ne na yi bayani akan inganta wadannan kayan aiki, ta hanyar gyara da abubuwa makamantan haka. Na kuma fara bayani akan hanyar sabuntasu, wato ajiye wani sashi na ribar daga lokaci zuwa lokaci domin sabunta su, abin da ake kira ‘Depreciation’ da Turanci. Na yi alkawarin karin bayani akan hakan, a makon da ya gabata, wanda zan yi a wannan makon. Zan kuma kara da bayani akan kasafin da ya kamata dan kasuwa ya ware domin bukatar kansa, da kuma wanda zai ware domin ‘Ko-ta- kwana’.  
Kamar yadda na yi bayani a baya, idan a misali a yau dan kasuwa ya sayi mota akori-kura domin tafiyar da harkarsa ta kasuwanci, sai ya kiyasta a cikin shekara nawa ne zai amfani wannan mota kafin karfinta yak are? Abin lura anan shine, karewar karfin mota ko na inji na kasancewa yayin da ta tsufa ko injin ya tsufa ya kasance kullum cikin gyara, ana ta kashe mata ko ana kasha masa kudi mai yawa, kuma ba a samun isasshen biyan bukata daga motar ko daga injin kamar yadda aka saba samu a baya; ba wai sai wannan inji ko mota ya tsaya ko ta tsaya gaba daya ba. Wato wannan kiyasi na batun a cikin shekara nawa ne za a iya amfanar abin gudanar da harka a cikin hayyacinsa? Kashe wa kayan aiki irin wadannan kudi da yawa fiye da kawar da babbar asara ce a kasuwanci. Sannan yawan tsayawarsu da kuma sauran matsalolin da za su haifar kamar rashin kuzari, su ma na iya jaza asara a harkar kasuwanci; domin wata rana ana ganin su za a nemi na kasuwa a biya domin samun biyan bukata.
To wannan kiyasi ya dogara da wane yanayi dan kasuwa ya sayi wannan mota: misali, sabuwa ya saye ta, ko kuma ja ce ya saye ta, ko kuma yar Kwatano ce? Wadannan yanayi na mota da na yi bayani guda uku su za su ba dan kasuwa alkiblar kiyasta shekarun da wannan mota za ta iya yi ana anfanarta. Misali, idan dan kasuwa ya sayi wannan mota sabuwa, a bisa shawara sai ya kiyasta amfaninta shekara biyar; in kuwa yar Kwatano ya saye ta, to ya kiyasta mata shekara uku. Idan ja ce ya saye ta, wato wani ya yi amfani da ita, to kiyasinta ya dogara da shawarar bakanike da kuma cewa shi wanda ya yi amfani da ita sabuwa ya saye ta ko kuma shi ma ’yar Kwatano ko jace ya saye ta? To koma yaya dai, kada dan kasuwa ya kiyasta shekarun da zai amfani jacen (gwanjo) mota ya wuce shekara biyu. A kuma lura cewa wannan misali da na ke yi da mota mota, za a iya kamanta shi da injunan tafiyar da harkar kasuwanci, kamar yadda na ambata a makalar baya a misalin kananan harkoki da ke amfani da injuna irin su gidajen bulo da na burodi da sauran makamantan su.
Sarari ba zai bar ni in misalta yadda za a yi amfani da kiyasi a kasafta ribar kasuwanci ba, domin ware kudin sabunta kayan gudanar da harka ba. Haka kuma ba zan samu sukunin bayani akan abin da dan kasuwa zai ware daga ribarsa ta kasuwanci domin bukatar kansa ba, da kuma wanda zai kasafta domin ‘ko- ta- kwana’ ba. Sai a kasance da ni idan Allah Ya kai rai mako na gaba.A wannan makon zan ci gaba da wannan makala ta Kasafta Ribar Kasuwanci da na fara makonni biyu da su ka gabata. A makon farko na fara bayanin yadda dan kasuwa zai kasafta ribar da ya samu daga harkarsa ta kasuwa a matsayin dabarar kasuwanci, inda na yi nuni ga dan kasuwa cewa babbar dabara ce gare shi  da ya ware wani kaso na ribar da ya samu domin kara karfin jarinsa. Na kuma shawarci dan kasuwa da ya ware wani kaso daga ribarsa domin inganta ko sabunta ko musaya injuna da motocin da ya ke amfani da su wajen tafiyar da harkarsa;   na kuma yi gargadi da jan hankali a makalar cewa ware kudi daga cikin ribar kasuwanci domin sabunta ko musaya motoci da injina da sauran kayayyakin tafiyar da harka ya zama dole domin a kullum karfinsu karewa ya ke yi yayin da ake amfani da su wajen tafiyar da harkar. Na kuma nuna  mahimmancin wannan al’amari, domin bukatar sabunta wadannan kayan aiki na iya samun dan kasuwa a lokacin da bai shirya ba, ya kuma saka shi a wani mawuyacin hali, yayin da wadannan ababen aiki suka kasa ba shi sukunin sayen wasu.
A makon da ya gabata ne na yi bayani akan inganta wadannan kayan aiki, ta hanyar gyara da abubuwa makamantan haka. Na kuma fara bayani akan hanyar sabuntasu, wato ajiye wani sashi na ribar daga lokaci zuwa lokaci domin sabunta su, abin da ake kira ‘Depreciation’ da Turanci. Na yi alkawarin karin bayani akan hakan, a makon da ya gabata, wanda zan yi a wannan makon. Zan kuma kara da bayani akan kasafin da ya kamata dan kasuwa ya ware domin bukatar kansa, da kuma wanda zai ware domin ‘Ko-ta- kwana’.  
Kamar yadda na yi bayani a baya, idan a misali a yau dan kasuwa ya sayi mota akori-kura domin tafiyar da harkarsa ta kasuwanci, sai ya kiyasta a cikin shekara nawa ne zai amfani wannan mota kafin karfinta yak are? Abin lura anan shine, karewar karfin mota ko na inji na kasancewa yayin da ta tsufa ko injin ya tsufa ya kasance kullum cikin gyara, ana ta kashe mata ko ana kasha masa kudi mai yawa, kuma ba a samun isasshen biyan bukata daga motar ko daga injin kamar yadda aka saba samu a baya; ba wai sai wannan inji ko mota ya tsaya ko ta tsaya gaba daya ba. Wato wannan kiyasi na batun a cikin shekara nawa ne za a iya amfanar abin gudanar da harka a cikin hayyacinsa? Kashe wa kayan aiki irin wadannan kudi da yawa fiye da kawar da babbar asara ce a kasuwanci. Sannan yawan tsayawarsu da kuma sauran matsalolin da za su haifar kamar rashin kuzari, su ma na iya jaza asara a harkar kasuwanci; domin wata rana ana ganin su za a nemi na kasuwa a biya domin samun biyan bukata.
To wannan kiyasi ya dogara da wane yanayi dan kasuwa ya sayi wannan mota: misali, sabuwa ya saye ta, ko kuma ja ce ya saye ta, ko kuma yar Kwatano ce? Wadannan yanayi na mota da na yi bayani guda uku su za su ba dan kasuwa alkiblar kiyasta shekarun da wannan mota za ta iya yi ana anfanarta. Misali, idan dan kasuwa ya sayi wannan mota sabuwa, a bisa shawara sai ya kiyasta amfaninta shekara biyar; in kuwa yar Kwatano ya saye ta, to ya kiyasta mata shekara uku. Idan ja ce ya saye ta, wato wani ya yi amfani da ita, to kiyasinta ya dogara da shawarar bakanike da kuma cewa shi wanda ya yi amfani da ita sabuwa ya saye ta ko kuma shi ma ’yar Kwatano ko jace ya saye ta? To koma yaya dai, kada dan kasuwa ya kiyasta shekarun da zai amfani jacen (gwanjo) mota ya wuce shekara biyu. A kuma lura cewa wannan misali da na ke yi da mota mota, za a iya kamanta shi da injunan tafiyar da harkar kasuwanci, kamar yadda na ambata a makalar baya a misalin kananan harkoki da ke amfani da injuna irin su gidajen bulo da na burodi da sauran makamantan su.
Sarari ba zai bar ni in misalta yadda za a yi amfani da kiyasi a kasafta ribar kasuwanci ba, domin ware kudin sabunta kayan gudanar da harka ba. Haka kuma ba zan samu sukunin bayani akan abin da dan kasuwa zai ware daga ribarsa ta kasuwanci domin bukatar kansa ba, da kuma wanda zai kasafta domin ‘ko- ta- kwana’ ba. Sai a kasance da ni idan Allah Ya kai rai mako na gaba.