✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da nake ba matasa hayar Keke NAPEP – Alhassan Gas 

Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Alhassan Abdullahi Saulawa wanda aka fi sani da Alhassan Gas, ya bayyana wa Aminiya cewa yana tallafa wa matasa…

Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Alhassan Abdullahi Saulawa wanda aka fi sani da Alhassan Gas, ya bayyana wa Aminiya cewa yana tallafa wa matasa ta hanyar ba su hayar Keke NAPEP ne su rika biya kadan-kadan don hana su zaman banza da saba musu da dogaro da kai.

“Na lura da cewa, jama’a sun yi wa gwamnati yawa musamman idan aka yi batun bayar da aiki. Idan muka dubi waɗanda suka kammala karatu tun daga sakandare zuwa jami’a kuma suke jiran aikin yi ga ƙarancin aikin. To sai na ga ya kamata a ce mu ’yan ƙasa mun yi wani abu don tallafawa,” inji shi.

“Shi ne na fara jarraba sayen babur mai taya uku Keke NAPEP domin bayarwa a riƙa yin haya. Da farko ana kawo kudin hayar da aka yi duk bayan kwana uku ko yadda muka daidaita. Kuma nakan canja wa mutum sabuwa bayan ɗan lokaci, idan na lura da irin ƙoƙarinsa.  Amma daga baya sai na sake tunani tunda na lura da yadda abin yake tasiri. Maimakon a ce kullum ko duk bayan mako  mutum  ya kawo balas, gwamma su rika biya kadan-kadan zuwa wani wa’adi har su biya kuɗin, domin ysu mallaki Keken baki daya. Abu kamar wasa, sai na ga matasan sun fara yin na’am da shirin. To in taƙaita maka a yanzu haka na bayar da sama da Keke 200 da ake aiki da su yanzu bisa wancan tsari,” inji shi.

Alhaji Hassan ya ce kafin wannan sana’a ta hayar babura, sayar da iskar gas na girki ya fara yi har ya yaye sama da mutum 100 da a yanzu suke dogaro da kansu. “Wadansu daga cikinsu sun yi gida sun yi aure, wadansu kuma mahaifansu suke taimakawa. Kuma a yanzu mun ƙara da babura. Kuma a  shekara biyar da na yi bisa wannan harka, har zuwa yau ni kaɗai ke tafiyar da harkokin ba tare da sa hannun kowa ba.  Sai da wadansu masu halin suka fara ganin fa’idar abin sun nemi mu yi haɗin gwiwa, to amma ka san mutum mai gaggawa ne, idan suka ji irin yadda muke yi sai su ce ba su iyawa,” inji shi.

Ya ce matsalar da ya riƙa samu da kuma ya yi zaton ita ta hana wadansu yin harkar ita ce, a wasu lokutan in Allah Ya kawo ƙaddara sai a ɗauki mugu wanda a ƙarshe in ba a yi sa’a, ba har mai abin hawan ake kashewa. To wannan ita ce babbar matsalar da wani lokaci ake fuskanta.

Da ya juya kan samun canji ta fuskar kasuwanci da sana’o’i a Jihar Katsina, Alhaji Hassan Gas ya ce, gaskiya yanzu ana samun ci gaba a jihar. Ya ce, suna ƙoƙarin kafa wata ƙungiya da za ta riƙa magana da murya ɗaya maimakon ƙungiyoyin daban-daban na ’yan kasuwa ko masu sana’o’in hannu.