Da Dumi Dumi

Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya rasu

Harabar Zauren Majalisar Jihar Nasarawa

Dan Majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Nasarawa ta tsakiya, Alhaji Suleiman Adamu, ya rasu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa dan majalisar ya rasu ne a daren Alhamis, 30 ga watan Afrilu, a asibitin gwamanti da ke garin Keffi bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya.

Dan majalisa mai wakiltar Udege/Loko, Alhaji Mohammed Okpoku ne ya fitar da sanarwar hakan ranar juma’a, yana cewa za a yi jana’izarsa da safiyar ranar juma’a, 1 ga watan Mayu.

Alhaji Sulaiman Adamu ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya