Search
Subscribe
‘Dan Sarki da ’yan mata hudu’ (2)

‘Dan Sarki da ’yan mata hudu’ (2)

Manyan gobe barkanmu da sake haduwa a wannan fili. Yau zan kawo muku karshen labarin da muka faro a makon jiya na Dan Sarki da ’yan mata hudu.’  Da fatan manyan gobe za su natsu don karanta yadda karshen labarin yake.

 

A cikin mata hudun Dan Sarki ya lura cewa ita babbar  tana da son girma domin ya gwada kona mata kaya da dutsen guga da gangan amma sai da ta mare shi saboda fushi.

Ta biyun kuma buri ya yi mata yawa kullum burinta shi ne ta auri Dan Sarki amma kuma tana da yawan son maza, ga yawo.

Ta ukun ba ta damu da auren Dan Sarki ba ita dai mai karamar buri ce kuma ba ta da raini. Domin akwai ranar da ta yi ado za ta fita, Dan Sarki yana wanke mota sai ya watsa mata ruwa, da ta fusata sai ta zage shi amma daga baya ta ba shi hakuri.

Ta hudun kuma ba ma za a sa ta a lissafi ba domin mata-maza ce. Sai son yin shigar maza da kuma wasa da maza.

Da Dan Sarki ya koma gida sai ya gaya wa mahaifinsa cewa ya samu matar aure. Haka aka kai gaisuwar neman aure gidan Hajiya Delu don neman auren ’yarta ta uku, aka yi aure. Sauran suka ji matukar takaici da ba su yi aikin alherin da Dan Sarki zai zabe su wajen aure ba.

Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi a wannan labari. Ya dace a koyaushe ku zama masu saukin kai da yin ladabi  da biyayya, hakan zai sa ku samu cin ribar rayuwa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin