Da Dumi Dumi

dan shekara 11 ya sanya hannu a kulob din Real Madrid

Joshua Pynadath, xan shekara 11 da ya sanya hannu a kulob din Real Madrid da ke Sifen.  A na iy a ganin hannunsa na dama daure da bandeji bayan ya samu rauni a yayin atisayeWanni yaro dan kimanin shekara 11 da da ke karatun sakandare a Kalifoniya kasar Amurka mai suna Joshua Pynadath ya sanya hannu a kulob din Real Madrid da ke Sifen.
Rahotanni sun tabbatar yaron shi ne irinsa na farko daga yankin Amurka da kulob din ya dauka wanda zai rika buga  wasa a matakin kanana (academy) kafin daga bisani ya koma matakin manya idan ya nuna kwazo.
Jushua, wanda ya kware a harkar kwallo, ana ganin babu kamarsa a daukacin Amurka a halin yanzu.  Matashi ne da ke wasa da kwallo (jugging) kamar aljani da ake ganin za a yi fama da shi nan gaba.
Tun farkon shekarar nan da muke ciki ne dai kulob din ya gayyaci yaron don yi masa gwaji, don haka a yanzu da kulob din ya gamsu da kwarewarsa ne ta sa ya gayyace shi don ya sanya hannu a kwantaragin shekara daya.
Ana sa ran kafin karshen wannan nan da muke ciki ne yaron tare da iyayensa za su koma Sifen don cigaba da zama.
Joshua Pynadath dai zai yi kwallo ne a kulob din matasa na Real Alebin A Team kafin ya samu hayewa mataki na gaba.
Shi dai Joshua tun tasowarsa a harkar kwallo babu wanda yake kauna da ya wuce Cristiano Ronaldo, yanzu mafarkin hadewarsa da dan kwallon ta tabbata tun da sun hade a kulob daya.
“A gaskiya na yi murna da na samu gayyata daga kulob din Real Madrid kuma mafarkina na haduwa da Cristiano Ronaldo ya tabbata”, inji Joshua a lokacin da yake hira da manma labarai.

Share