Da Dumi Dumi

Dan takarar Sanatan APC ya fadi a rumfar Buhari

Dan takarar Sanata a mazabar Katsina ta Arewa a jam’iyya mai mulki ta APC Ahmad Baba Kaita ya fadi a rumfar zaben Shugaba Muhammadu Buhari’s da ke unguwar Sarkin Yara Ward A, da rumfar zabe ta Kofa Baru (03), da rumfar zabe ta Gidan Niyam duk a karamar hukumar Daura da ke jihar Katsina.

Jam’iyyar Accord Party (AP) ce ta lashe zaben rumfunan.

Jam’in zaben Aliyu Abdullahi ya sanar da sakamakon  zaben sanatocin kamar haka: Dan takarar APC Ahmad Baba Kaita ya samu kuri’u 247, dan takarar PDP Mani Nasarawa ya samu kuri’u 2, yayin da dan takarar AP Mohammed Lawal Nalado ya samu 262.

A bangaren sakamakon ‘yan takarar Shugaban kasa, shugaba Buhari ya lashe rumfar zabensa da kuri’u 532 yayin da dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya samu kuri’u 3.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya