Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Darasi ga masu kin amincewa da auren dole

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole

Masu bibiyar wannan shafi ina yi muku sallama irin ta addinin Musulunci, assalamu alaikum. Da fatan an yi bikin Sallah lafiya bayan an kammala azumin Ramadan.  Na san tuni wadansu suka kare azumin Sitta Shawwal yayin da wadansu kuma suke kan yi.  Fatarmu dai  Allah Ya sada mu da alherinSa duniya da Lahira, amin.

Yau kuma zan tabo wani labari ne da ke sosa zuciya ko kuma ci mana tuwo a kwarya musamman ga samari da ’yan matan wannan zamani.

Ba wani abu ba illa abin da ake kira AUREN DOLE!!!

Me ake nufi da auren dole?  A takaice auren dole na nufin yi wa budurwa ko saurayi aure ba da amncewa ko saninsa ba. Ma’ana, aure ne da wadansu iyaye kan tilasta wa budurwa ko saurayi su auri wanda ba sa so.  Amma hakan ya fi kasancewa a kan mata fiye da maza. Kafin ka samu namijin da iyayensa suka yi wa auren dole sai ka ga an yi wa mata fiye da 20, don haka da zarar an ambaci auren dole abin da ya fi daukar hankali shi ne budurwa aka yi wa auren dolen.

Sai dai a wannan labarin zan tabo yadda wadansu iyaye ne suka yi wa dansu namiji auren dole, ba tare da sani ko amincewarsa ba.

Na kawo wannan labari ne don ya zama darasi ga masu kin amincewa da auren dole don akwai darasin da za a dauka a wannan labarin musamman ga samari da ’yan matan wannan zamani.

Ga yadda labarin ya kasance:

A wani gari ne a Arewacin kasar nan (ba zan ambaci suna ko jiha ba) aka yi wani magidanci Malam Usman tare da matarsa Hajiya Delu.  Sun dade da yin aure amma Allah bai ba su haihuwa ba, sai daga baya.  Daga baya ne Hajiya Delu ta haifi namiji da suka sanya masa suna Ibrahim. Kuma tun daga lokacin ba su sake samun haihuwa ba. Hakan ya sa suka nuna wa dan so da kauna ta hanyar yi masa tarbiyya tagari.  Hasali ma tun yana karami suka sanya shi a makarantar allo da ya dan tasa ne suka kai shi makarantar boko (zamani).

Mu kwana nan

 Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805