✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diphtheria ta yi ajalin yara 4 a Kano

Kazalika, wasu yara 28 sun kamu da cutar a karamar hukumar.

Akalla yara hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar diphtheria a Karamar Hukumar Minjibir a Jihar Kano.

Jami’in yada labaran Karamar Hukumar, Mista Tasiu Yahaya ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kano.

Yahaya, ya kuma ce yara 28 kuma sun kamu da cutar.

“An tabbatar da mutuwar yara hudu yayin da wasu 28 suka kamu da cutar Diphtheria a Karamar Hukumar Minjibir ta Jihar Kano.

“Yaran 28 sun kamu da cutar a garuruwan Kwarkiya, Kuru, Kunya da Minjibir.

“Shugaban rikon kwarya na Karamar Hukumar, Muhammad Yakubu Kunya, ya yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki da su gaggauta kai wa Karamar Hukumar Minjibir dauki.

“A nasa bangaren, hakimin karamar hukumar, ya bukaci sarakunan gargajiya da malamai da su tashi tsaye wajen wayar da kan al’umma tare da yin addu’ar samun sauki daga cutar,” in ji sanarwar.

Kakakin Ma’aikatar Lafiya na jihar, Abdullahi Ibrahim, ya ce an mika lamarin ga daraktan kula da lafiyar jama’a don yin bincike kafin tabbatar da lamarin.