Search
Subscribe
Dole matasa su kawo sauyi a harkar siyasa  – Tukur Bodinga

Dole matasa su kawo sauyi a harkar siyasa  – Tukur Bodinga

Dan Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar Karamar Hukuma Bodinga ta Kudu Alhaji Tukur Bala Bodinga ya ce ba ya da burin da ya sanya a gaba da ya wuce cika wa mutanen da suka zabe shi alkawarin da ya dauka, domin ya shiga siyasa ce saboda ya kawo al’umma ci gaba mai dorewa.

Tukur ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya inda ya ce ya shiga siyasa ce domin ta zama wajibi gare shi in ba su shiga ba, za a ci gaba da samun bara-gurbi a madafun ikon kasa wadanda ba ruwansu da jama’ar da suka zabe su.

“An bar matasa baya a cikin harkar jagoranci dole ne mu tashi mu kawo sauyi ga harkar siyasa da wakilcinmu, abu guda biyu ne tafiyar da jagoranci da yadda wakilci da wanda ya kamata mutane su zaba,” inji shi.

Ya bai wa magoya bayan jam’iyarsu ta APC tabbacin samun kyakkyawan jagoranci da samun nasara a shari’un da ake yi daga sama har kasa da yardar Allah.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin