✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ebola na ci gaba da barna a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo

Cutar nan da ita ma take illanta mutum cikin sauri kamar HIB, wato Ebola tana ci gaba da barna a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, bayan kididdiga…

Cutar nan da ita ma take illanta mutum cikin sauri kamar HIB, wato Ebola tana ci gaba da barna a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, bayan kididdiga ta nuna cewa daga watan Yuli zuwa yanzu akalla mutum 170 sakamakon kamuwa da cutar.

Wannan bayanin kididdigar ya fito ne daga Ma’aikatar Lafiyar kasar, inda ta ce sakamakon cutar da ta fara bulla a Arewacin Kibu sannan ta shiga Ituri, an samu kusan mutum 329 suna zubar da jinni a jikinsu, wanda yana daya daga cikin manyan alamun cutar.

Daga cikin wadannan mutane, an tabbatar 294 na dauke da cutar kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Ya zuwa yanzu mutum 170 ne suka mutu, sannan sama da mutum 100 sun warke daga cutar.

Hakazalika akwai mutum 35 da suka mutu bayan da aka ga suna zubar da jinni, sai dai ba a tabbatar ko Ebola ce ta yi ajalinsu ba.

Kuma sakamakon yadda aka binne mutanen ba tare da an yi gwajin me ya kashe su ba, ya sanya ba a samu cikakken bayanan musabbabin mutuwar tasu ba.

A wani gangamin da aka fara a yankin a watan Agusta, an yi wa mutum dubu 28 da 727 allurar rigakafi.

Sannan kuma bincike ya nuna cewa zubar da jinin da aka gani a wannan karon ya haura na shekarar 1976 da cutar ta fara bulla.

A shekarar ta 1976 mutum 318 ne suka zubar da jinni, sannan 280 daga cikinsu suka mutu.

A 1976 ne cutar Ebola ta fara bulla a duniya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, sannan a watan Disambar 2013 ta yadu a wasu kasashen Yammacin Afirka.

A tsakanin 2014 da 2017cutar ta kama kusan mutum dubu 30 a kasashen Gini da Laberiya da Saliyo, inda sama da mutum dubu goma sha daya daga cikinsu suka mutu.