✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadada tunani na kara habaka kasuwanci – Dokta Yusuf

Wani masanin harkokin kasuwanci kuma malami a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa Dokta Muhammad Yusuf ya ce, “Fadada tunani na kara kawo ci gaban kasuwanci.” Malamin…

Wani masanin harkokin kasuwanci kuma malami a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa Dokta Muhammad Yusuf ya ce, “Fadada tunani na kara kawo ci gaban kasuwanci.”

Malamin ya bayyana hake ne a wajen bude bikin baje kolin Manya da Matsakaita da Kananan Masana’antu domin inganta kasuwanci a tsakanin mata.

Bikin baje kolin an bude shi ne a ranar Asabar din makon jiya a Katsina Motel wanda ya samu halartar masu ruwa-da-tsaki kan abin da ya shafi harkokin kasuwanci da bunkasa shi.

Dokta Muhammad ya ce, akwai abubuwa da dama da duk dan kasuwa zai zama yana da su da za su ba shi damar habaka kasuwancinsa, “Da’a da girmamawa na daga cikin abin da kasuwanci ke bukata daga dan kasuwa. Kazalika zamanantar da kayan kasuwancin na kara wa harkar daukaka da ci gaba,” inji shi.

Ya kuma kawo misali da yadda yanzu ake yin ganyen shayi da  ganyen zogala da ganyen yakuwa da citta da sauransu. Kuma ya kawo  misalin cewa ta hanyar wani bincike da ya gudanar ga masu kananan sana’a, inda ya ce ya je garin Kaita wajen wata mai yin kuli-kuli, bayan ganin irin yadda take yi, sai kuma suka ba ta shawarar ta rika zuba shi a cikin leda wanda hakan ya janyo mata karin kasuwa. Ya ce a Batsari sun samu matar da take yin man kadanya da sauransu. “Lura da yanayi da irin zamanin da ake ciki da lura da irin kayan da masu saye ke saye a wannan lokacin yana daga cikin abin da ya kamata mai kasuwanci ya yi la’akari da su,” inji shi.

Shi kuwa Malam Abdurrahman Sabi’u Rafindadi, malami a Kwalejin Ilimi ta Yusuf Bala Usman da ke Daura, ya yi bayani ne a kan yadda addinin Musulunci ya yi nuni a yi a kasuwanci. Malamin ya kara wa mahalarta taron kwarin gwiwa a kan yadda matar Ma’aiki (SAW) ta zamo tana kasuwanci tun ma kafin Annabi (SAW) ya aure ta, inda ya ce ’yar kasuwa ce wadda ake cewa ba a san yawan jama’ar da ke tafiyar mata da harkokin kasuwancinta ba a wancan lokaci saboda irin yadda ta rarraba kayan kasuwancin.

Sai ya ja hankali kan cewa yana da kyau dan kasuwa ya kiyaye yin algushu a kasuwancinsa ko yin amfani da bataccen abu.  Ya ce dan kasuwa ya san cewa zai amfanar da kansa da iyalansa da kuma sauran al’umma a wajen gudanar da kasuwancinsa.

A jawabin maraba, Shugaban Kungiyar Masu Kananan Masana’antu ta Jihar Katsina, Alhaji Yahaya Sodangi ce wa ya yi, “Harkokin kasuwanci su ne kan gaba kuma na farko a harkokin rayuwar dan Adam. Don haka yana da muhimmacin a karfafa wa wadanda suke kokarin kawo sababin abubuwa da kokarin ganin sun samu karbuwa a abin da sika kawo,” inji shi. Alhaji Sodangi ya kara da cewa yana daga cikin kokarin da suke yi na fadakarwa tare da zamanantar kananan masana’antu.

Bikin baje kolin wata kungiya mai suna,”New Faces New Boices” a karkashin jagorancin Shugabar Kungiyar ta Kasa A’ishatu Debola Aminu ta shirya ta hannun wakiliyar kungiyar a Jihar Katsina Hajiya Hadiza Bashir Aliyu, kamar yadda Babbar Sakatariyar Kungiyar wadda ta wakilci Shugabar, Barista Yetunde Okafor ta ce. Ta kara da cewa yana daga cikin manufofin kungiyar ganin ta ciyar da harkokin bunkasa tattalin arziki da ciyar da masu masana’antu gaba ta hanyar bunkasa kasuwancinsu.

Ta ce, “Na yi farin cikin ganin cewa wannan kudiri na wannan kungiya tuni kwalliya ta biya kudin sabulu a tsakanin kasashe 18 da kungiyar take gudanar da harkokinta. Wannan kuma wata dama ce ta ganin cewa ana samun musayar ra’ayi da haduwa da sababbin abubuwa wadanda babu tantama za su ciyar da kananan sana’o’i na Afirka gaba.”

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ciniki da Masana’antu da Yawon Bude-Ido Alhaji Abubakar Yusuf cewa ya yi, akalla akwai ma’adanan da ba a taba ba kusan 36 a Najeriya. Sannan yana daga cikin manufofin gwamnatinsa Masari don ganin ta habaka harkokin kasuwanci da ganin jihar ta sake maido da sunan da aka santa da shi shekaru aru-aru da suka wucem fadada harkokin kasuwanci. Gwamnan ya tabbatar wa mahalarta bikin baje kolin goyon bayan jihar tare da ba su duk wata gudunmawar da ta dace. Kwamishinan wanda ya yi jawabi mai tsawo kan muhimmacin sana’a, musamman ga mata, ya ce yana da kyau kungiyar ta kara fadada harkokinta har a cikin karkara domin a can ne masu kananan sana’o’i suka fi yawa.

Wakiliyar kungiyar ta jiha Hajiya Hadiza Bashir Aliyu ta ce ta yi kokarin kawo wannan biki ne a Arewa musamman a Katsina bisa lura da ta yi cewar dukan yawace-yawacen da suka yi a kungiyar matan Arewa ba su wuce a kirga su ba. Hadiza ta ce za ta yi duk iya kokarinta don ganin mata da suke zaune a karkara sun amfana da harkokin kungiyar.

Mafi yawan kayan da aka baje kolinsu a wajen bikin kaya ne wadanda aka yi na gida. Akwai sarrafaffun kayan abinci da kayan kwalliyar mata da zannuwa da sauransu. Har ila yau akwai batun kiwon zuma da zomo da kifi da sauransu da aka kawo a wajen bikin.