✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta haramtawa Siasia shiga harkar wasanni

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da tsohon kocin Najeriya Samson Siasia saboda samunsa da laifin yin magudin wasa tare da karbar cin…

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da tsohon kocin Najeriya Samson Siasia saboda samunsa da laifin yin magudin wasa tare da karbar cin hanci don bai wa wasu dama su yi nasara.

Siasia ya zamo kocin Najeriya daga shekarar 2010-2011 sannan kuma na wani dan lokaci a 2016, ba a bayyana lokacin da ya aikata wannan laifin ba, amma a ranar 11 ga Faburairu 2019 aka kammala binciken laifin tsohon kocin.

Siasia, ya kuma taba kasancewa kocin ‘yan wasan Najeriya ta ‘yan kasa da shekara 20 da kuma 23.

A sanarwar dakatarwar da FIFA ta fitar na cewa, an samu Siasia da laifin “amincewa ya karbi na-goro domin sauya sakamakon wasanni.”