✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta karyata zargin da ake yi mata na sanya Ajantina a rukuni mara zafi a gasar cin kofin duniya

A shekaranjiya Talata ne Hukumar FIFA ta karyata zargin da wasu suke mata na da gangan ta sanya kasar Ajantina a rukunin da ba shi…

A shekaranjiya Talata ne Hukumar FIFA ta karyata zargin da wasu suke mata na da gangan ta sanya kasar Ajantina a rukunin da ba shi da zafi don ganin kasar ta haye rukunin na gaba a gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.
Mai magana da yawun Hukumar Mista Delia Fisher ce ta karyata wannan zargi.
Ta ce babu kanshin gaskiya a labarin da ake bazawa na cewa Hukumar FIFA ta yi coge a lokacin da aka yi jadawalin gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Ajantina dai za ta fafata ne da kasashen Iran da Najeriya da kuma Bosnia-Herzegobina al’amarin da wasu ke ganin babu tantama Ajantina ce za ta yi zarra a  rukunin.
Wasu sun yi tambayar ta yaya kasar za ta zabi garin Belo Horizonte a matsayin sansanin horar da ’yan wasanta tun kafin a gudanar da jadawalin gasar idan ba ta da masaniyar yin cogen sannan bayan an gudanar da jadawalin sai ta kasance a garin za ta zauna don yin wasa na farko da kasar Iran?
Tuni Ajantina ta yi watsi da wannan zargi inda ta nuna an gudanar da jadawalin ce a bisa tsarin babu cuta, ba cutarwa.