✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta yi wa NFF ta’aziyyar rasuwar Isaac Promise

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta yi  Hukumar NFF ta Najeriya ta’aziyyar rasuwar tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta ’Yan kasa da shekara…

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta yi  Hukumar NFF ta Najeriya ta’aziyyar rasuwar tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta ’Yan kasa da shekara 20 (U-20) Isaac Promise.

Isaac ya rasu ne a Amurka kamar yadda shugaban kulob din Austin Bold FC na Amurka Mista Bobby Epstein ya sanar a ranar Alhamis ta makon jiya.

Isaac ya rasu yana da shekara 31 kuma ya yi kwallo a kulob da dama da suka hada da Genclerbirligi da Trabzonspor da ke Turkiyya kafin ya koma kulob din Austin Bold na Amurka.

Ya taba yi wa kungiyar Super Eagles kwallo.

Ya rasu ne bayan ya kamu da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka.

A kan haka ne FIFA ta aika wa Najeriya sakon ta’aziyya a shafin sadawarta na Twitter, inda ta jajanta wa ’yan uwa da iyalan mamacin da Hukumar NFF game da rasuwar dan kwallon.