✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitattun mutum 10 da suka rasu cikin mako daya a mace-macen Kano

Tun lokacin da mace-macen mutane ta auka wa Birnin Kano, kimanin mako biyu da suka gabata al’umma jihar ke ta rasa ’yan uwa da abokan…

Tun lokacin da mace-macen mutane ta auka wa Birnin Kano, kimanin mako biyu da suka gabata al’umma jihar ke ta rasa ’yan uwa da abokan arziki, lamarin da ya dasa tsoro da firgici a zukatansu.

A makon jiya Aminiya ta ruwaito rasuwar mutum 150 cikin mako daya, yayin da zuwa yanzu aka tabbatar mata ana binne gawa akalla 40 zuwa sama a kullum a makabartun birnin. Sai dai abin da ya fi jan hankalin mutane a wadannan mace-mace shi ne yadda a tsakanin kwana uku kacal aka rasa wadansu fitattun ’ya’yan jihar da suka hada da farfesoshi da manyan malaman jami’a da manyan ma’aikatan da suka rike mukamai da dama a jihar da kasa baki daya.

Ga 10 daga cikin fitattun mutanen da suka rasu cikin mako daya:

Farfesa Sabo Sulaiman Kurawa:

An haifi marigayi Sabo Kurawa a Unguwar Kurawa a 1949. Ya shiga Firamaren Kurmawa da Kwalejin Horon Malamai ta Wudil. Daga nan ya samu digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya. Sannan ya yi digirinsa na biyu da na uku a Jami’ar ilIinious a Amurka. Ya yi aiki a Jami’ar Bayero a matsayin malami tun daga 1978 zuwa 2014, a Sashen Nazarin Zamantakewar Dan Adam. Ya kuma rike mukamai da dama da suka hada da Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Bangaren Koyarwa da Gudanarwa, kuma ya taba rike mukamin Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU). Ya rasu ya bar matar aure daya da ’ya’ya shida.

Farfesa Aliyu Umar Dikko:

An haife shi a birnin Kano. Ya yi firamare da sakandare duk a Kano. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a ABU Zariya. Daga nan ya je Jami’ar Sheffield da ke Amurka. Ya fara aiki a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkkwato a 1986 daga baya ya samu canjin wurin aiki zuwa Jami’ar Bayero, a Sashen Koyar da Aikin Likita. Ya rike mukamai daban-daban a jami’ar.

Dokta Muhammad Uba Adamu

Shi ne mahaifin Shugaban Jami’ar Karatu-Daga-Gida ta Najeriya (NOUN), Farfesa Abdallah Uba Adamu. An haifi marigayin a 1935. Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar ABU kafin i ya tafi Jami’ar Indiana a Amurka, inda ya yi digiri na biyu. Daga nan ya yi digiri na uku a Jami’ar Bayero. Ya yi aikin koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Kano. Ya taba rike mukamin Shugaban Kananan Hukumomin Birni da Dambatta a lokacin mulkin soja.

Farfesa Balarabe Maikaba

Malami a Sashen Koyon Aikin Jarida na Jami’ar Bayero Kano. Ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero Kano. Ya kuma yi digirinsa na biyu a Jami’ar Ibadan, inda ya dawo daga baya ya ci gaba da koyarwa a jami’ar Bayero, har ya samu digirinsa na uku. Ya rike mukamai da dama a jami’ar. Ya rasu a ranar Lahadi 26 ga Afrilu 2020, bayan ya yi gajeriyar jinya. Akwai bayanan da suka ce dama can yana fama da ciwon suga.

Farfesa Ibrahim Ayagi

Shi ne mammalakin Makarantar Hassan Gwarzo da ke Kano. Shi kuma ya rasu a ranar Asabar 25 ga Afrilu 2020 bayan ya yi fama da zazzafan zazzabi. Sai dai Aminiya ba ta samu labarin cewa ko yana da wani ciwo a can baya ba. An haife shi a 1940. Ya yi karatunsa na firamare da sakandare a Kano. Ya yi digirinsa a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya a Sashen Tsimi da Tanadi. Sannan ya tafi wata jami’a a kasar Amurka, inda ya yi digirinsa na biyu. Ya yi aiki a wurare da da ama ciki har da Gidan Rediyon BBC, kuma ya taba zama shugaban kwamitin tattalin arziki na kasa.

Musa Tijjani

Fitaccen dan jarida ne da ya yi Editan jaridar Triumph da ke Kano. Daga baya ya zama Editan jaridar mako ta Leadarship. Shi ma ya yi fama da zazzabi, inda bayan ya shafe mako guda a asibiti ya ce ga garinku nan.

Sheikh Tijjani Tukur Yola

Fitaccen malamin addinin Musulunci ne wanda kafin rasuwarsa shi ne Limamin Masallachin Murtala da ke Hausawa a Kano. Marigayin mai kimanin shekara 85, ya yi fama da ’gajeriyar jinya, inda ya rasu ranar Litinin 27 ga Afrilu 2020.

Malama Halima Shitu

Marigayiya Malama Halima Shittu

Fitacciyar malamar addinin Musulunci ce, tana daga cikin matan da suka fara yin tafsiri a Kano. Ita ce uwargidan Sheikh Abdulwahab Abdullah. An haife ta a 1963. Ta yi karatun firamare da sakandare a Kano. Lokacin da maigidanta ya tafi karatu Madina sai ya tafi da ita, inda ta samu Diploma a harshen Larabci. Daga baya ta je ta yi digiri a fannin Alkur’ani da Hadisi. Kafin rasuwarta, Malama Halima Shitu ita ce Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta Afirka reshen Najeriya. Ta rasu ta bar ’ya’ya shida.

Alkali Rabi’u Dahiru:

Tsohon Alkalin Alkalan Jihar Kano, ya rasu ranar 25 ga Afrilu 2020 bayan ya yi fam a da gajeriyar jinya.

Dokta Ghali Kabir Umar:

Ya rasu ranar 27 ga Afrilu 2020. Kafin rasuwarsa, malami ne a Sashin Zane-Zanen Gidaje a Jami’ar Kimiyya da Sanaa ta Wudil. Duk da cewa Aminiya ba ta samu bayani kan matsayin lafiyarsa ba, amma an samu rahoton cewa ya yi fama da rashin lafiya na takaitaccen lokaci kafin rasuwarsa.

Akwai fitattun mutane da dama da suka rasu a Kano ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Alhaji Adamu Ahmed Sarawa wanda aka fi sani da Adamu Atamas wanda ya rasu yana da shekara 66 bayan gajeriyar jinya a gidansa da ke Kano da wani manajan banki da mahaifiyar fitaccen jarumin nan Ado Gwanja da sauransu da dama.

Kuma muna cikin hada wannan rahoto ne muka samu labarin rasuwar mahaifin Ko’dinetan Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da Cutar Kurona Dokta Sani Aliyu, Alhaji Aliyu Daneji a birnin Kano. Danda Alhaji Mahmud Daneji ya ce ya rasu ne a shekaranjiya Larabayana da shekara 95 inda aka yi jana’izarsa jiya Alhamis.

Yawancin wadanda suka rasu dai sun manyanta, kuma wadansu suna da tarihin rashin lafiya da suke da ita, amma yawancin mutanen jihar suna zargin mace-macen na da alaka da cutar Kurona. Gwamnatin Jihar ta ce tana sane da mace-macen amma ta ce ba su da alaka da cutar Kurona. Sai dai ta ce za ta binciki mace-macen, inda ta ce kwamitin yaki da cutar Kurona zai yi kokarin tattara alkaluman mutanen da suka rasu, don gano musabbabin rasuwar tasu. Jama’a dai sun zuba ido su ga abin da sakamakon binciken zai nuna.