✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani makiyaya za su ci gaba da kisa matukar Buhari na kan mulki – Atiku

Dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ce kashe-kashen da Fulani makiyaya da suke dauke da makamai za su ci gaba…

Dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya ce kashe-kashen da Fulani makiyaya da suke dauke da makamai za su ci gaba da gudana sai masu zabe sun sauke Shugaba Buhari daga mulki a zaben Fabrairu mai zuwa.

Atiku Abubakar ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani kan rahoton Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar kan rikicin manoma da makiyaya a Najeriya, inda rahoton ya ce gwamnati ta gaza magance rikicin wanda ya jawo mutuwar mutum  3, 641 a  cikin shekara uku.

Wta sanarwa da Kakakin Atiku, Mista Phrank Shaibu ya fitar, ta ruwaito tsohon Mataimakin Shugaban Kasar yana bayyana martanin Fadar Shugaban Kasa kan rahoton a matsayin “tafiyar hawainiya”.

Ya ce “Matukar ’yan Najeriya ba su yi waje da gwamnatin APC ba kashe-kashen da Fulani makiyaya suke yi  za su ci gaba kuma a karshe za su haifar da husuma mai girman gaske a tsakanin kabilun kasar nan.

“A bayyane take yanzu cewa gwamnatin Buhari, kamar yadda Amnesty ta fada, ta gaza wurin kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya wadanda suka dade suna fuskantar tashin hankali iri-iri wadanda za a iya guje musu, kuma hakan yana barazana ga kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya,” inji Atiku.

Atiku ya kara da cewa wadannan rikice-rikicen suna tsoratar da ’yan kasashen waje masu zuba jari a Najeriya. “A koyaushe idan aka samu rikici sai gwamnati ta sha alwashin kamawa da hukunta masu laifi daga bisani sai hakan ta kuma faruwa sannan gwamnati ta kuma maimaita alwashi. Wannan abin tsoratarwa ne ga al’ummar kasa da kuma ’yan kasuwa na kasashen waje.

“Saboda haka, duk da irin kokarin da suka yi, Buhari da APC ba za su iya tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin ’yan Najeriya ba game da rikicin Fulani da makiyaya da ke daidaita al’umma da kasa baki daya,” inji shi

Atiku ya ce abin Allah wadai ne da gwamnatin ta Buhari ba ta dauki wani mataki ba game da rahoton Bankin Duniya kan cewa Najeriya tana kan hanyar zama wani babban fage inda matasa ’yan kasa da shekara 18 ke mutuwa a ka-a kai.