Da Dumi Dumi

Fulani yanzu kamar wadanda ruwa ya ci ne – Miyetti Allah

Alhaji Usman Baba Sakataren Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Kasa (MACBAN)
Alhaji Usman Baba Sakataren Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Kasa (MACBAN)

Alhaji Usman Baba Ngelzarma shi ne Babban Sakataren Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Kasa (MACBAN), Aminiya ta tattauana da shi  kan jingine shirin Gwamnatin Tarayya na kafa RUGA da satar jama’a don neman kudin fansa a cikin al’umma da wasu batutuwan:

A baya al’ummar Fulani makiyaya sun fuskanci matsalar satar shanu, sai ga shi yanzu kuma ana samun wadansu daga cikinsu suna satar mutane don neman kudin fansa, yaya kuke ji?

Wannan abin takaici ne, sai dai mun san akwai wani bangare na kafofin watsa labarai da na al’umma da ba sa son kasar nan ta zauna lafiya musamman a karkashin wannan gwamnatin inda suke danganta duk wani abu da ya faru mara kyau da Fulani tun kafin a tantance, ba don komai ba sai don kasancewar Shugaban Kasar Bafulatani ne. Misali a sauran abubuwa ana kiran mai laifi da sunan laifinsa, amma idan abin ya kasance Bafulatani ne ya aikata, sai su danganta lamarin da daukacin al’ummar Fulani makiyaya. Sananne ne cewa matsalar ta’addanci ko na batagari bai bambance kabila ko addini, illa idan manufar masu aikata wa ta zo daya, sai ka ga ana samu daga kowace al’umma.

Sannan akwai ’yan siyasa da ke amfani da bambancin addini ko kabilanci suna hada kai da wadannan kafofin watsa labarai don kawai su nuna cewa babu wani abin alheri da ke gudana a karkashin wannan gwamnati.

Me kake gani ya jawo yawaitar shigar Fulani cikin masu satar mutane?

ADVERTISEMENT

Gaskiya akwai matasan Fulani da suka shiga cikin wannan fitinar ta satar mutane ana neman kudin fansa kamar yadda ake samu daga wasu kabilu. A nazarin da muka yi a kungiyance mun gano cewa matsalar ba ta rasa nasaba da dadaddiyar rigima da aka rika samu a tsakanin Fulani makiyaya da manoma da aka gaza magance ta har zuwa yau inda lamarin ya gawurta ya rikide ya koma matsalar tsaro a kasa baki daya. Da farko ya faro ne daga matsalar satar shanu wadda su Fulanin nan su ne suka fi kowa jin jiki. Sai yanzu ya koma satar mutane ko fashi, wanda shi din ma dai Fulani makiyayan su ne suka fi jin jiki a lamarin, illa dai nasu labarin bai bayyana saboda a cikin daji ake yi musu kuma ba su san hanyoyin sadarwa na zamani ba kamar sauran al’umma bare a ji. Kafin ka ji sanarwar sace mutum guda a cikin gari, an sace Fulani sama da 10 a cikin dazuka amma ba a ji. A dauki ’ya’yansu ko matansu a tilasta musu biyan kudi. A wani zubin ba ma satar ake yi ba, waya kawai za a buga musu a ce an san komai game da kai, su gargade ka cewa idan ba ka kai musu kudi ba zuwa lokaci kaza, za su zo har rugar da kake, su kashe ka. Wani zubin rugar za su zo, su buga waya su ce ko ka ga wuta da ke ci ta baryi kaza da rugarka, to su bakinka ne, su umarce ka ka yanka musu dabba ka zo musu da shi za ku ci tare kuma a yi muhawara a kan yadda za ka kwaci kanka da iyalanka. Wani zubin jaka za su aika maka, su ce sun ba ka zuwa lokaci kaza ka cika musu ita da kudi za su fada maka inda za ka kai musu. Wannan ya sa makiyaya sun yi ta sayar da shanunsu don biyan kudin fansa. Al’umma ce da ba ta san wata sana’a ba idan ba ta kiwo ba. Ilimin addini ma ba su tsaya suka yi ba bare na boko da ba ya kusa da su. Ga matsalar yaduwar miyagun kwaya da ta makamai a tsakanin al’umma. Ka ga ke nan duk wata al’umma da ta samu kanta a cikin wannan hali na tsaka-mai-wuya, komai na iya faruwa. Wadansu kuma talauci ne da rashin aikin yi, wadansu sa su aka yi, wadansu dama suna cikinta, ba dai irin wanda babu. Fulani sun yi asarar shanu sama da miliyan biyu da ya jawo rashin abin yi ga iyalai da dama.

A wani lokaci kuma zalunci da ake yi musu a bangaren hukuma ta taimaka. Duk lokacin da suka fuskanci matsala a tsakaninsu da manoma, idan aka kai maganar gaban hukuma don raba fada, maimakon a dubi kiyasin barnar da dabbobi suka yi sai a bukaci makudan kudi na fitar hankali daga wajen makiyayi. Kuma dama ka san filayen nan na kiwo da burtali da ake bi don kaiwa gare su, mafi yawansu yanzu babu su, sakamakon bukata ta noma ko gini da karuwar al’ummar ke ci gaba da haifarwa, sai hakan ya sa kullum sai an fuskanci rigima da ba lallai ba ne a yi adalci wajen warware ta.

Ga sababbin garuruwa da gine-ginen gwamnati kamar makarantu da sauransu, sannan a gefe guda su kansu dabbobi nan karuwa suke yi a kullum sakamakon karuwar bukatarsu da ake yi alhali filayen kiwon nan nan raguwa suke yi. To tarin wadannan matsaloli sun haifar da rashin fahimta a tsakanin makiyaya da manoma inda ta kai kusan daga kowace kabila makiyayi yana da abokin gaba, saboda ba kabilar da ba za ka samu manomi a cikinta ba. Wannan da sauran abubuwan da na lissafa sun taru sun yi wa makiyaya dabaibayi. Sai ka ga idan an kama ’yan fashi ko masu garkuwa da mutane, sai a samu ’ya’yan al’ummarmu da yawa a ciki. Sannan su kansu jami’an tsaron nan abubuwa sun taru sun yi musu yawa, sai ka rasa da wanne za su ji saboda gwamnatocin baya sun gaza samar da maslaha a kan lamarin tun yana karami, ga shi yanzu muninsa na neman ya ci kowa.

Sai dai alhamdulillahi daga baya bayan nan an fara samun sauki a lamarin. Idan ka duba Jihar Zamfara da nan hanyar Kaduna kullum sai nasara ake ta samu kuma abin ya lafa, sannan ita kanta gwamnati na duba yadda za ta taimaki wannan al’umma ta sama musu mafita don ta magance matsalar daga tushe.

Gwamnatin Buhari ta yi yunkurin killace makiyaya a wuri guda a matsayin maslaha da kuma inganta rayuwarsu, sai dai a duk yunkurin ta fuskanci turjiya, me za ka ce?

Ita gwamnati idan aka ce ta siyasa ce, to ta zama ta jama’a, kuma a duk lokacin da korafi ya yi yawa a kan wata manufarta dole ta saurara. Sama da shekara 30 ke nan ba wata gwamnati da ta waiwayi matsalar nan sai a yanzu da Gwamnatin Buhari ta yi yunkuri. To sai ya zamana shi kuma ya gamu da kalubalen siyasa a kan wannan al’amari ba don komai ba sai don adawa ta siyasa da abokan hamayyarsa suka kara zafafawa da rurutawa kasancewarsa Bafulatani. Su kuma suna wadannan abubuwan ne don ganin sun hana gwamnatinsa yin duk wani abin kirki har zuwa karshen wa’adinta don su samu abin fada wa jama’a, wannan al’ada ce ta siyasa.

Sai dai fa ba haka abin yake ba a kasashen da suka ci gaba. Saboda mancewa ake yi da dukkan wasu bambance-bambacen siyasa bayan zabe, a rungumi gwamnati gaba daya don ganin ta samu nasarar yi wa al’ummar kasa aiki. Sai dai kash! Mu a nan Najeriya ba haka abin ya ke ba. Ci gaba da yakarta ake yi tare da yi mata mummunan fata har ta kare wa’adinta, wannan abu na farko ke nan. Na biyu idan ka dubi siyasar Buhari, daya daga cikin manofofinsa shi ne yakar cin hanci da zalunci. Yana kuma samun nasara a kan haka inda aka karbi dimbin dukiya daga wajen wadansu tare da toshe hanyoyin da ake bi wajen yin wannan satar. Hakan ya sa ya samu makiya ta ko’ina, kuma suna iya kokarinsu wajen ganin ya gaza ta kowace fuska, ta hanyar amfani da wasu kafofin watsa labarai da kungiyoyi da ’yan siyasa inda suke ta iza wutar rigima. To idan gwamnati ta zama ta siyasa ce kuma mai sauraron jama’a, ka ga dole ta dakata har a nemo wata maslahar.

Mu dai a kungiyance mun ja baki mun yi shiru in ba yanzu da nake magana da kai, ba don komai ba sai dai don ganin ba a ma fara abin ba, kuma ba mu san inda lamarin zai kai ga al’ummarmu ba idan gwamnati ta doge a kan sai ta yi. Fulani makiyaya a yau tamkar wadanda yaki ya ci ne, ko takobi ka jefa masa kamawa zai yi. Saboda haka a shirye muke a kungiyance mu rungumi duk wani tsari da gwamnati ta kawo mana ba don komai ba sai don ganin halin da al’ummarmu ta tsinci kanta a ciki, da ya maida ita mafi shan wuya fiye da kowace kabila. Rikicin satar shanu bai bar su sun zauna lafiya ba, rikicinsu da na manoma bai bar su sun zauna lafiya ba, ga na cin zali na a tsare su a kan hanya ana karbar makudan kudi daga hannunsu, ga na satar mutane, ga musgunawa daga bangaren jami’an tsaro ga na sarakuna ga kuma na cikin gida a tsakanin kungiyoyinsu na makiyaya. Matsaloli dai ta ko’ina ga su nan. Wannan ya sa ba mu da wani zabi a kan duk wani abu da gwamnati ta tsara mana illa mu runguma wanda a baya ba wata gwamnati da ta yi yunkurin haka yau sama da shekara 30 ke nan, sai a yanzu a wannan mulki na Shugaban Kasa Buhari.

A Kudu maso Gabas, gwamnoninsu sun fitar da sanarwar hana ware wurin kiwo ko kai dabbobi ta kasa, yaya kuka ji da wannan doka?

Mu dai mun san cewa a hukumance kasar nan ta al’ummarta ce gaba daya kowa na iya zuwa bangaren da yake so don zama ko sana’a matukar bai kuntata wa abokan zamansa ba, kamar yadda doka ta bayyana. Wannan shi ya sa Fulani makiyaya ke a ko’ina a bangaren Yarabawa da Ibo kamar yadda ake samun dan kabilar Ibo a duk wani kauye na nan Arewa. Wannan shi ne ’yancin da kasa ta ba kowa kuma ba a kebe Bafulatani ba. A dalilin haka muna goyon bayan al’ummarmu da ke can su zauna a wadancan yankuna matukar ba za su tsangama wa abokan zamansu ba. Idan suka tsangwama to ba ma tare da su saboda mu muna shugabantar Fulani makiyaya ne da ke neman halaliyarsu ta kiwo da suka gada, ba ma tare da marasa gaskiya ko masu neman rigima. Batun hana shanu tafiya ta kasa kuwa yana bukatar karin tattaunawa tare da nema wa lamarin mafita daga bangaren Gwamnatin Tarayya. Kuma muna kira ga gwamnati ta dawo da tsarin da ta jingine na Ruga ko kawo wani abu a madadinsa don aiwatarwa a jihohin da suka amince a yi musu kamar yadda ta tallafa wa dukkan sana’o’i na al’ummar kasar nan. Wannan shi ne adalci ga kowa, kuma na tabbata sauran jihohin da suka ki yarda da tsarin, da kansu za su zo su nemi a yi musu shi.

 

Share