Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

FURE: Labarin Uwargida Farida (31)

Jim kadan bayan tafiyar mutumin nan, Saratu da kawarta Binta sun samu kansu cikin kadaici. dakin ya yi tsit, domin kuwa dukansu biyu sun shiga tunani, ba tare da sun sake yin wata magana da juna ba. Daga bisani ne Binta ta dan karkata kai, ta kalli fuskar kawarta, amma ga alama ita ba ta ma san abin da take ciki ba.

ADVERTISEMENT

“Saratu, yaya na ga fuskarki duk ta canja? Ga alama kina cikin damuwa.” Binta ta tambayi kawarta.

Saratu ta nisa sannan ta yi gyaran murya. “Ke dai bari, anya kuwa ba mu tafka babban kuskure da muka zo nan ba?”

ADVERTISEMENT

“Wane irin kuskure kuma?”

“Na lura da wasu alamomi, wannan mutumin ba malamin Allah da Annabi ba ne. Ke ba ki lura da yanayin gidan nan ba? Me ya sa za su amsar mana kudi tun ma kafin mu gana da malamin?”

“Ni ban gane inda kika nufa ba,” inji Binta.

 “Ni abin da na fahimta, wannan mutumin da za mu gani, ba malami ba ne, boka ne.” Saratu ta fadi haka a yayin da ta karkato fuskarta ta fuskanci kawarta.

“Da malamin Allah ne da ba haka za mu ga tsarin gidansa ba. Kamata ya yi mu ga almajirai suna daukar karatu a daidai wannan lokacin.”

“To, ni dai matar da ta yi mini kwatance da shi, ta ce aikinsa na ci. Iyaka abin da zan iya kararwa ke nan. Kuma in ban da abinki, ina ruwanki da koma wane ne shi, ai biyan bukata ake so…”

Saratu ba ta bari kawarta ta ci gaba da magana ba, sai ta dakile ta. “Ta yaya za ki ce ina ruwana, to idan ba ruwana me ya kawo ni nan? Ni fa ban zo da niyyar kawo matsalata ga boka ba, domin na riga na san sharrinsu. Babu wani alheri a tattare da boka.” 

Cikin bacin rai take wannan magana, tare da haka kuma ta dan daga muryarta, wanda haka ta sanya Binta ta razana.

“Haba, haba Saratu! Don Allah ki daina daga murya, ki kwantar da hankalinki. Wannan al’amari bai kai nan ba, mu hakura mu ga karshen gudun ruwan tukunna.”

 A daidai wannan lokacin ne suka ji motsin dawowar wannan mutumi da ya ajiye su nan dakin. Bayan ya shigo sai ya ce musu su tashi ya kai su wajen malamin. 

“Amma kuna ji na? Shi fa malam ba ya son gardama, duk abin da ya ce muku, ku amince da shi. Muddin dai kuna son biyan bukatar abin da kuka zo nema, to ku bi sharuddan Malam sau-da-kafa.” Mutumin nan ne yake jaddada musu sharuddan malamin nasa, Magana yake kasa-kasa cikin murya mai taushi da jan hankali.

A daidai lokacin da yake maganar nan, sai Saratu da Binta suka kalli juna ba tare da cewa uffan ba. Sun dai mike daga kan kujerunsu, sun bi shi zagai-zagai a baya.

Koda suka shiga dakin da malamin yake zaune, sun same shi a zaune kan wata shimfidar tabarma, wacce aka dora wani jan kyalle a samanta. Shi kuwa yana sanye da doguwar farar jallabiya da farar hula a kansa.

“Assalamu alaikum,” inji Binta.

Malamin bai amsa mauu sallamar ba, ya yi shiru gum abinsa, kamar wani kurma. Ya dai saki dogon hannunsa ya yi musu ishara da wata tabarma da ke shimfide a gabansa. “Ku zauna, ku zauna.”

“Cikinku wace ce Saratu?” Ya tambaya cikin wata murya mai cike da jiji-da-kai.

“Ni ce,” inji Saratu.

“An shaida mini cewa ke ce mai bukatar aikina, ita wannan ’yar rakiya ce. Don haka ke ki koma can dakin amsar baki, bari in saurare ta.”

Lokacin da Binta ta mike za ta bar dakin, sai Saratu ta shiga fargaba, kirjinta ya yi ta bari. Ita ma sai ta mike kamar za ta bi bayanta.

“Koma ki zauna, ita na ce ta fita ba ke ba!” Umurnin da ya ba Saratu ke nan, a lokacin da ya ga alamar za ta tashi. Ita kuma sai ta ji kamar an kama hannunta an zaunar da ita. Nan take ta koma ta zauna, duk da cewa ta rasa natsuwa. Idanuwanta sun kada suka yi ja kamar barkono, fuskarta ta yi fari kwal kamar fatalwa. 

Cikin minti uku ta bayyana masa abin da take bukata. “Babu abin da nake so illa a taimaka mini da rokon Allah, Alhaji Baba ya amince da ni, ya aure ni.”

Tana gama bayaninta, shi kuma sai ya dauki lokaci yana wani zane-zane a kan wani rai-rai fari tas da ke zube a kan wani faifai. Bayan ya kammala sai ya kalli idanuwanta kai tsaye. “Tashi ki matso nan gabana!” 

Saratu ta kidime, tsoro ya kara kama ta. 

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!” 

Kalmomin da ta yi ta maimaitawa ke nan a cikin zuciyarta.

“Ko ba ki jina ne? Na ce tashi ki matso kusa da ni, akwai abubuwan da zan duba ne a jikinki, kafin in san matakin da zan dauka domin samar miki da bukatarki.”

Ba ta san lokacin da ta tashi ta matsa kusa da shi ba. Shi kuma ya tashi tsaye, ya kama tafin hannunta, ya duba dukan yatsunta daya-bayan-daya. Ya sanya hannunsa na dama kan goshinta, ya tsaya haka na dan lokaci. Daga bisani ya koma ya zauna.

“Ki mike kafafunki.”

Ya kama yatsun kafafunta ya dudduba, sannan ya koma kan shimfidarsa ya sake zama. Ya dauko farin yashin nan ya ci gaba da zane-zane. Daga nan ya nisa, ya aje faifan, ya dago kai ya kalle ta cikin ido kai-tsaye.

“Na karanta dukan matsalolinki kuma tuni na tanadi hanyoyin magance su. Abu guda zan gaya miki, kada ki yi kokwanto kuma kada ki yi gardama ko musu; duk abin da na bukaci ki aikata, ki aikata kawai.”

Ita dai Saratu ta yi kasake tana kallonsa kuma tana jin dukan abin da yake gaya mata. Daga bisani ya jera mata wasu bayanai tare da wasu bukatu da wasu sharudda. “Ki je ki shirya, nan da jibi ki dawo nan!”

***

Ba Saratu ta samu kanta ba, sai da ta ga ta fito daga dakin mutumin nan. Ba ita ta samu kwanciyar hankali ba sai da ta ga ta hadu da kawarta a dakin jiran baki. Koda ta zo ta same ta, cikin sauri ta uzzura mata suka fita daga gidan malamin nan. Hankalinta a tashe ta uzzura wa Binta cewa su tafi bakin hanya kawai su shiga mota, domin komawa gida. 

Binta ta yi kokarin cewa ta ba ta minti biyu domin ta je ta yi ban-kwana da malamin, amma ta hana ta.

“Ke mu tafi kawai. Wallahi ba zan kara ko minti daya a gidan nan ba!”

Haka suka kama hanya a kasa, suka tunkari bakin hanya, inda za su shiga motar zuwa Kano. Suna tafiya, suna ci gaba da magana.

“Ke kuwa yaya na ga duk kin ta da hankalinki haka, shin ko ba a dace ba ne?”

“Ai wallahi na yi nadamar zuwa wurin bokan nan. Ba malamin Allah ba ne, matsafi ne!”

“Tsafi kuma?” Binta ta tambaya, a yayin da ta kama bakinta cikin mamaki.

“Idan ba matsafi ba, kin ji abin da ya gaya mini kuwa? Cewa ya yi nan da kwana biyu in dawo ni kadai. Ya ce in yi kokari in debo masa kasar sawun Alhaji Baba. Ban da wannan kuma wai in taho masa da ruwan zam-zam. Daga karshe ya nuna mini karara cewa idan na zo, zai aske mini gashin hammata da gashin gabana, wai da su zai hada ya ba ni maganin.”

“Subhanallahi!” Binta ta fada cikin mamaki.

“Wallahi ba zan kara zuwa nan ba, ba zan kara cusa kaina ga halaka ba. Zan tafi in roki Allah Ya sama mini mafita.” Saratu tana huci, har da tuntube ta diga aya ga maganarta.

Za mu ci gaba