✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gara in yi karamar sana’a da in yi bara – Tsoho Mai Tallar Biro

   A’isha Buhari ta tallafa masa da jari Malam Adamu Muhammad dattijo ne mai kimanin shekara 75 da ke Unguwar Gayawa a Karamar Hukumar Ungoggo…

  •    A’isha Buhari ta tallafa masa da jari

Malam Adamu Muhammad dattijo ne mai kimanin shekara 75 da ke Unguwar Gayawa a Karamar Hukumar Ungoggo a Jihar Kano kuma mutum ne mai himma wajen neman na kansa. Kullum yana fita sana’arsa ta sayar da biro da maka, wadda dududu ba ta wuce jarin Naira dubu biyu ba.

Da wannan sana’ar yake tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum shi da iyalansa. Ganin cewa ya tsufa amma ya ce ba zai yi bara ba, gara ya yi karamar sana’a da karamin jari. Duba da yanayin da yake ciki ne ya sa matar Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari ta ba shi tallafin Naira dubu 250 domin ya ci gaba da kula da kansa kuma ta yi masa alkawarin wani tallafin da zai zauna a waje guda domin gudanar da sana’arsa.

Aminiya ta gana da Malam Adamu dangane da al’amuran rayuwarsa ta yau da kullum.

 

Takaitaccen tarihina

An haife ni a garin Gayawa, Karamar Hukumar Ungoggo, Jihar Kano kuma zan kai akalla shekara 75. Ina da ’ya’ya takwas da mata daya kuma tun ina yaro na taso na samu a gidanmu ana sana’ar noman lambu kuma ni ma na yi wannan sana’ar tun ina karami. Haka kuma na yi sana’a iri-iri daga ciki har da dillanci a kasuwannin Kurmi da ke can Kudancin Najeriya. Na yi sana’ar gini, inda har na kai ana ce min helman. Dayake sana’ar lambu muke yi kuma muna girma ga shi gari yana ci mana gonakin, duk sun zama fulotai wasu an sayar, wasu kuma na ’yan uwane sun karbi abinsu.

Lokacin da na ga wajen da muke nomawa duk sun zama gidaje sai na koma Birnin Kebbi na sami wata gona nake yin aikin lambu, tun da na saba. Abin da na noma sai in kawo wa iyalaina. To kuma girma ya kama ni, ga shi yarana ba su girma sosai ba. Sai na dawo gida domin waccen gonar ba za ta nomu ba.

Da na dawo gida, babu wani abin yi takamaimai, sai na sa gidana a kasuwa na sayar da shi na kama haya, na ci gaba da yin sana’a. A kwana a tashi sai jarina ya kare.

 

Tsufa ya kama ni amma na saba da neman na kaina   

Lokacin da na ga jarina ya kare kuma karfina ya kare sai na fara sayar da maganin gargajiya soboda in ci gaba da rayuwa, ni da iyalaina. Ina zuwa kasuwannin kauye ina tallar maganin gargajiya sai na ji yawon ya ishe ni, sai na yi tunani in samu wata karamar sana’a wacce zan dinga yi ina samun rufin asiri. Sai na fara sana’ar sayar da ‘biro’ da ‘maka’ kuma jarin bai wuce Naira dubu 2 ba,  ga shi ina da ’ya’ya kanana kuma suna zuwa makaranta. Shi ne na ci gaba da yin sana’a. Kullum ina zuwa kan titin Magwan da ke kan hanyar zuwa Gidan Gwamnati, domin hanya ce ta ’yan boko kuma ina dan ciniki daidai gwargwado.

Ga shi girma ya kama ni amma ni na saba da neman na kaina. Ni dai ba zan wulakanta kaina ba in rika rokon mutane domin yana jawo mutuwar zuciya.

 

Yadda aka yi na samu tallafi daga A’isha Buhari

Ina cikin sana’ata, to ashe wasu mutane suna la’akari da ni kuma suka turo aka yi hira da ni a wajen da nake yin sana’ata kuma aka haska ni a gidan talabijin. Sai Malam Mukhtar ya ce min Hajiya Fauziya ce ta turo shi domin ya tattauna da ni. Kawai wata rana ina zaune sai na ji an yi sallama da ni aka ce wai matar Shugaban Kasa ce ta yi min aike, ta gan ni awajen sana’ata kuma ta tausaya mini, ga kudi Naira dubu 250 in yi jari. Gaskiya na yi murna kwarai da gaske kuma ina yi mata godiya sosai, Allah Ya saka mata da alheri, Allah Ya taimake ta, ita da maigidanta domin sun taimake ni kwarai da gaske kuma zan ci gaba da kokarin neman na kaina in sha Allahu.

Uwargidan Shugaban Kasa ta yi min alkawarin bude mini shago domin in ci gaba da sana’ata a ciki, domin in huta yawo da nake yi a cikin gari kwararo-kwararo.

 

Yadda zan saraffa jarin da A’isha Buhari ta ba ni

Zan yi kokarin amfani da jarin wajen sayar da kayan masarufi a shago, domin ni ma in samu in huta da yawo kuma domin in kula da iyalaina, musamman ’ya’yana masu zuwa makaranta kanana. Zan rika zuwa kasuwar Singa ina saro kaya ina sayarwa a hankali har ta Allah ta kasance. Allah Ya taimake mu kuma Ya saka wa Hajiya Fauziya, ita da matar Shugaban Kasa, A’isha Buhari.

Iyalan Malam Adamu

Lokacin da wakilinmu ya ke zantawa da iyalan Malam Admu, daya daga cikin ’ya’yansa mai suna Zainab mai shekara 15, ta ce tana son komawa makaranta.

“Shekarata biyu ke nan ina zaune a gida ba na zuwa makaranta saboda mahaifina ba shi da halin da zai biya mini kudin makaranta kuma ni ina so in yi karatu, ni ma domin in taimaki al’umma kamar yadda yanzu aka tallafa wa babana. Kuma in dai zan samu tallafin karatu zan koma makaranta ni ma in yi ilimi. Ba na so a yi mini aure ban gama karatu ba. Ajina uku a sakandare na daina zuwa saboda rashin kudin makaranta. Yanzu ’yan ajinmu sun shiga aji biyar a sakandare, ni kuma ina gida a zaune.”

Malam Adamu ya ce “Ni ma ina so ’ya’yana su yi ilimi amma wallahi ba ni da halin da zan biya musu. Ka ga yanzu jarin da aka ba ni, idan na biya kudin makaranta da shi ka ga zan koma gidan jiya kuma ba na so na ga iyalaina cikin yunwa. Shi ya sa nake so in yi sana’a kamar yadda uwargidan Shugaban Kasa ta ba ni jari amma duk da haka zan rika biya wa wasu kuma ina neman a tallafa mani, domin da na kowa ne, musamman ita Zainab yarinya ce mai kokari. Duk abin da aka koya mata, nan da nan za ta iya shi, tana zuwa ta daya a jarabawa.

 

Wakilin Gidauniyar Fauziya D. Suliaman

Da yake tattaunawa da wakilin Aminiya, Malam Mukhtar Harun Aminu, wanda shi ne wakilin Gidauniyar Fauziya D. Sulaiman ya bayyana cewa shi ne wanda ya fara ganin mutumin a bakin Danjar Magwan da ke kan hanyar zuwa Gidan Gwamnatin Kano. Ya ce “kullum idan na wuce sai in ga wannan dattijon yana sana’ar sayar da biro da maka. Sai wata rana na tsaya na tambaye shi a kan sana’ar da yake yi. Na ce baba wannan sana’ar da ita kake rayuwa? Ya ce ita ce sana’arsa kuma da ita yake daukar nauyin iyalansa. Sai na tambaye shi ko idan ya samu jari zai inganta sana’ar tasa? Sai ya ce ai gida zai zauna kuma ya fara harkar kayan masarufi, ya samu ya huta, domin girma ya kama shi kuma ba shi da manyan ’ya’ya.

“Wannan ta sa na garzaya na shaida wa Hajiya Fauziya D. Sulaiman sai ta turo mu muka yi hira da shi ta musamman, aka haska a gidan talabijin na Arewa 24. Daga nan kuma saka hirar a shafinta na zumunta na Isntagram. A nan ne matar Shugaban Kasa ta gani kuma ta turo masa da tallafin Naira dubu 250, sannan ta yi alkawarin sama masa shago da zai zauna ya dinga sana’a a ciki, ya huta zirga-zirga domin tsufa ya kama shi, kusan shekararsa 75.

 

Shawarar Malam Adamu ga al’umma da gwamnati

Maimakon a dinga tsangwamar masu bara a kan hanya, musamman tsofaffi, a samu wasu su karfafa musu gwiwa da sana’a. Domin wasu watakila a da sun yi sana’a sai jarin ya kare kamar yadda ta faru a kaina. Ba kowa ba ne zai yi tuninin ya ci gaba da sana’a ba, domin yana ganin ya tsufa. Amma da mutane suna karfafa musu gwiwa ta hanyar ba su jari da kula da su, to za a iya samun saukin barace-barace a kan tituna da tsofaffi suke yi.

Ita kuma gwamnati, ya kamata ta samu ta dinga ba tsofaffi horo na musamman a kan sana’ar da za su yi dagaro da kansu, sannan a ba su jari. Tabbas, idan gwamnati ta na yin wannan, to za a rage yawan barace-barace a kan tituna da tsofaffi suke yi.

 

Burinsa na karshe a rayuwa

Babban burina a rayuwa shi ne in mallaki muhalli nawa na kaina, domin ba na so in mutu in bar iyalaina cikin halin haya. Sannan ’yata Zainab, ina son ta yi karatu kamar yadda take tsananin son karatu, ni kuma ga shi ba ni da halin daukar nauyinta. Domin ba ita kadai ba ce, akwai kannenta kuma duk ni nake daukar nauyinsu.

Domin cika burina na mallakar muhalli, a yanzu daga wannan tallafin kudin da A’isha Buhari ta ba ni, zan yi jarin ci gaba da sana’a, zan rika ajiye kudin da zan rika samu na riba, har in sayi fili in fara gini a hankali. Idan kuma na samu wani cikin al’umma ya taimaka mani da shi, to sai in ce burina ya cika ke nan.