✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da Mutane: Muna rayuwa cikin tashin hankali – Shugabannin garuruwan da ke titin Kaduna-Abuja

Al’umma mazauna kan titin Kaduna-Abuja na rayuwa cikin wani mawuyancin hali na tsaro da damuwa, kasantuwar rashin tsaro da ya yi kamari a kan titin.…

Al’umma mazauna kan titin Kaduna-Abuja na rayuwa cikin wani mawuyancin hali na tsaro da damuwa, kasantuwar rashin tsaro da ya yi kamari a kan titin.

Tun lokacin da rashin tsaro ya karu a kan hanyar, tilas mazauna yankin suka canza yanayin rayuwarsu domin kuwa wasunsu sun sha fadawa hanun masu garkuwa da mutane kuma sai da suka biya kudin fansa sannan aka sako su, wadansu  kuma  rayuwarsu suka rasa gaba daya.

Babban abin damuwa kuma shi ne yadda masu kananan sana’o’i a kan hanyar suka kaurace wa sana’o’in nasu saboda ta’azzarar rashin tsaro a hanyar, da kuma rashin ciniki.

Dagacin Fada Achi, Mista Ayuba Dodo Dakolo

Sannan kuma babban dandalin sayar da gasassun kaji da ke garin Kakau, yanzu babu shi saboda masu zuwa saye duk sun kaurace wa yankin, shi ma saboda tsoron masu garkuwa mutane don amsar kudin fansa.

Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin ya fahinci cewa ayyukan masu satar mutane domin neman kudin fansa ya matukar gurgunta cin kasuwar dare a wannan hanya baki dayanta. Abin ya yi muni a garin Rijana, kasantuwar cewa akasarin mazauna yankin wadanda manoma ne, duk sun kaurace wa gonakinsu. Kadan daga cikinsu ke yin ta maza har su shiga gonakin nasu amma fa iyalansu na cikin damuwa har sai sun komo gida lafiya.

Dagacin Fada Achi da ke garin na Rijana, Mista Ayuba Dodo Dakolo ya ce rashin tsaro a yankin nasu ya shafi tattalin arzikin garin, domin akasarin mutanensu manoma ne kuma da shi suka Dogara.

“A yanzu duk mutanenmu na cikin damuwa saboda ba mu iya zuwa gona kuma noma shi ne abin da muka sani kaka da kakanni.

“A matsayina na basarake a garin nan, a kullum ina kira ga al’ummarmu da kuma na Fulani da ke cikinmu da kada mu bari wasu daga waje su zo su yaudare mu, har mu cutar da juna,” inji shi.

Sai dai wani abin damuwa a garin shi ne, akasarin Fulanin da ke garin na Rijana sun rasa shanunsu, wasu kuma sun koma noma amma duk da haka su ma masu satar mutanen ba su kyales u ba.

”Wadannan mutane ba su kyale mu ba duk da kasancewar mu Fulani. Haka kuma jami’an tsaro ba su kyale mutanenmu ba, domin da sun zo kama wanda ake zargi sai su kama Fulani, hakan na damun mu,” inji shi.

Wasu daga cikin mazauna kauyukan da ke kan hanyar da suka gana da wakilinmu sun ce a wasu lokuta suna ganin bata garin na shigowa cikin gari a kan babura amma ba su iya kama su saboda tsoro.

A garin Doka ýsu ma lamarin bai canza ba, domin asibitin da ke kan hanyar wanda kuma aka samar da shi saboda taimaka wa mutanen yankin da ke zagaye da wajen, yana cikin wani hali na rashin kayan aiki da kula.

Binciken Aminiya ya gano cewa likitocin da aka tura aiki wajen ba su son zuwa saboda tsoron bin hanyar. Majiyarmu a asibitin ta ce hakika suna aiki cikin tsoro a asibitin saboda babu wata katanga a bayan asibitin domin hana bata gari shigowa kuma ga shi jeji ne babba a bayan asibitin har zuwa dajin Birnin Gwari.

Ya ce marasa lafiya wasu lokuta suna kwana ne su kadai cikin asibitin ba tare da ma’aikatan ba har zuwa washegari domin kowa na cikin tsoro da damuwa.

Haka kuma mazauna kauyen Kurmin Kare ýda ke kusa da garin Katari sun ce duk da kasancewar garinsu na tsakiyar inda ake ta’asar ne masu satar mutane ba su taba shigowa kauyen ba sai dai kawai su tare matafiya a titi.

Sarkin garin Kurmin Kare, Maiwada Dogonyaro ya yi kira ga gwamnati ne da ta dauki matakin da ya dace domin magance matsalar domin kuwa ba su jin dadin zama ko kwanciyar hankali a yankiný sannan kuma ayyukan masu satar mutane na bata sunan garin nasu.

A kauyen Kufewa, akasarin mazauna garin sun yi kaura, domin a farkon shekarar nan ne ’yan fashi da makami suka kai hari garin tare da sace masu dukiya. Ya ce da yawan ’yan garin da suka koma sun tarar da an kwashe masu kayan abinci da sauran abubuwa da suka gudu suka bari .

Sarkin kauyen wanda a yanzu yake gudun hijira a garin Rijana mai suna Ayuba Audu ya ce ya yi gudun hijira ne shi da mutanensa saboda rashin tsaro. Ya ce akalla mutanensa bakwai aka kashe lokacin da ’yan bindigan suka shigo kauyensu. “Ni da mutane ne dole muka yi hijira muka bar garin, ba don muna son yin hakan ba. Mun gudu mun baro kayan abincin da muka noma kuma ko da matasanmu suka koma sai suka tarar duk an sace kayan noman da muka noma,” inji shi.

Ga alama mazauna kauyukan da ke kan babbar hanyar Kaduna-Abuja na cikin damuwa domin ba su ga alamar tsaro zai inganta a hanyar ba nan da ’yan lokuta kadan masu zuwa, kasantuwar kaurace wa hanyar da masu ababen hawa suke yi a kullum