Search
Subscribe
Gidauniyar Jama’a Foundation ta shirya taron shan ruwa

Wasu daga mahalarta liyafar buxe bakin

Gidauniyar Jama’a Foundation ta shirya taron shan ruwa

A ranar Lahadin da ta gabata ce Gidauniyar ‘Ya’yan Masarautar Jama’a (Jama’a Foundation) ta shirya bikin shan ruwa karo na biyu a dakin taro na Dubu Ebent da ke cikin garin Kafanchan, inda ta gayyaci shugabannin kabilun Yarbawa da na Igbo da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da shugabannin addinai.

Lokacin da yake gabatar da jawabin maraba, shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Abdullahi Zubairu, Sarkin Fadan Jama’a, ya ce ganin irin nasara da kuma natijar da suka samu a sanadiyyar irin wannan walimar cin abincin da gidauniyarsu ta shirya a bara ne tsakaninsu da wadanda suka gayyata ya sa a bana suka kara fadada lamarin inda suka shigo da sauran bangarorin.

Yace idan aka koma ga irin zamantakewar da aka gudanar a baya, tsakanin Musulmi da Kirista wajen mu’amala da ziyartan juna zai haifar da fahimtar juna da kuma ci gaba. A cewarsa, ta hanyar zaman lafiya ne ake samun kowane irin ci gaba.

Ya ce rashin kusantar juna na daya daga cikin abubuwan da ke gurgunta zaman lafiya, inda yace a yanzu kungiyarsu ta tashi haikan wajen yin amfani da irin wannan wata mai girma da sauran lokuta don kulla zumunci da kuma jaddada kira kan hadin kai da zaman lafiya a aikace.

Da yake jawabi a madadin bangarorin jami’an tsaron da suka halarci zaman, kwamandan ‘yan sandan kwantar da tarzoma da ke Kafanchan (62 Skuadron), Yusuf Muhammed Lawal ya yaba wa gidauniyar bisa irin wannan hobbasan, inda kuma ya yi kira ga kungiyar da ta rika sanya mata a irin wannan gayyatar bisa la’akari da irin muhimmancin da su ke da shi a cikin al’umma.

Kwamandan ya kuma yi kira ga mahalarta irin wannan liyafa da su rika isar da sakon da ke ciki idan sun koma ga al’ummarsu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin