✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar tankar fetur ta halaka mutum 2 da kona motoci 8 a Jos

Wata gobara da ta tashi a lokacin da ake sauke man fetur daga wata motar tanka, a wani gidan mai da ke kan hanyar Bauchi…

Wata gobara da ta tashi a lokacin da ake sauke man fetur daga wata motar tanka, a wani gidan mai da ke kan hanyar Bauchi a garin Jos, Jihar Filato, a daren ranar Juma’ar da ta gabata; ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 2 tare da kona motocin tanka guda 4 da kananan motoci   guda 4.

Wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 11:30 na dare, a lokacin da ma’aikatan gidan man suke kokarin sauke mai daga wannan motar tanka zuwa wata motar tankar ta daban.

Majiyar ta ce wannan gobara ta tashi ne a lokacin da injin bayar da wutar da suke amfani da shi ya kama da wuta, a inda ya yi sanadin tashin gobarar, wadda ta kone wani mai gadi a gidan man mai suna Malam Isah da wani yaron babbar mota da take gidan, a lokacin da gobarar ta tashi.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa a lokacin da wannan gobara ta tashi ta kone kananan motoci guda 4 da motocin tanka guda 2 kurmus, a yayin da wutar ta shafi motocin tanka guda 2.

Wani mai gadi da yake makwabtaka da wajen da wannan gobara ta tashi, ya yi bayanin cewa jami’an kashe gobara sun kwashe awa kamar 6 suna kokarin kashe gobarar, kafin su sami nasarar kashe ta.