✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe Katsina za ta samu Maga-isa

Gobe Asabar ce Mai martaba Sarkin Katsina zai nada Alhaji Ibrahim Sambo wanda aka fi sani da Ibrahim Magnet a sarautar Maga-isan Katsina. Sabon Maga-isan…

Gobe Asabar ce Mai martaba Sarkin Katsina zai nada Alhaji Ibrahim Sambo wanda aka fi sani da Ibrahim Magnet a sarautar Maga-isan Katsina.

Sabon Maga-isan an haife shi a 1955, kuma ya yi firamare a Unguwar Shanu Kaduna, daga nan ya wuce Sakandaren gwamnati da ake kira a yanzu da Kwalejin Dikko da ke cikin garin Katsina. Tsohon ma’aikacin lafiya a babban asibitin Katsina daga 1978 zuwa 1982, Magnet ya fada harkokin kasuwanci bayan ya ajiye aiki da babban asibitin inda ya fara da kafa wani kamfani mai suna Sambo International, daga bisani kuma ya sake bullo da Magnet Oil and Gas har zuwa ga Magnet Farms da kuma wata gidauniyar da ake kira Ibrahim Magnet Foundation.

A ganawarsa da Aminiya a Katsina, Ibrahim Magnet ya ce nadin na gobe shi ne sarauta na takwas da ya samu daga masarautu daban-daban. Ya ce sarauta ta baya-bayan da aka ba shi ita ce, ta Maga-isan Katsina wadda Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi masa a ranar 18 ga watan Agustan bara.

“Ita wannan sarauta ta Maga-isan Katsina, ni ne na farko da aka sake yi wa ita bayan shekara 100 da suka wuce a zamanin marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Kafin ita wannan sarauta daga masarautar ta Katsina, ina rike da sarautar Garkuwan Matasan Arewa wadda marigayi Sarki Kabir Usman Nagogo ya nada ni. Kazalika sarautar Maga-isa kamar yadda tarihi ya nuna, sai wanda ya isa ga komai a wajen al’umma shi ne ake yi wa ita. To ina jin kila saboda wadannan dalilai a fahimtata domin ba mu yi magana da Sarki ko wani ba, amma ina zaton su ne dalilan da suka sa Sarki ya ga ya dace a ba ni wannan sarauta,” inji shi.

Maga-isan ya ce, sauran dalilan sun hada da lura da Sarkin ya yi na cewa, Magnet ya isa ga aiwatar da duk wani aikin taimako da jinkai ko kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma ta fuskoki daban-daban. “Na lura cewa, Mai martaba yana lura da irin rawar da nake takawa musamman a wajen wasan Polo wanda za mu ce daga gidansu aka gaje shi a kasar nan. An yi karancin ruwa a filin wasan wanda za a shayar da dawaki, ni ne na gina rijiyoyin burtsatse a filin. Sannan duk wani abin da na lura da shi ana bukata kafin a ce me, na sa an yi. Kuma a can baya, bayan nadin Garkuwan Matasa da masarautar ta Katsina ta yi mini har ila yau, ta nada ni a matsayin “Uban Nakasassun Jihar Katsina.”

Game da ayyukan sarautar ta Maga-isan, ya ce, “Ina cikin ’yan Majalisar Sarki amma ba masu zama na yau da kullum ba, ni mashawarci ne kuma ina cikin wadanda za su rika wakiltar Sarki a duk wani wurin da aka gayyace shi ko aka neme shi. Kuma zan iya zuwa wajen Sarki kai- tsaye, saboda waccan isar da na yi gare shi. Wannan kadan ne daga cikin matsayi da ayyukan wannan sarauta tawa.”

Ba masarautar Katsina ce kadai ta yi wa Ibrahim Magnet sarauta ba, ita ma masarautar Daura ta yi wa Maga-isan Katsina sarautar Jakadan Hausa tun a shekarar  2017. Ita ma wannan sarauta ta ba shi damar wakiltar Mai martaba Sarkin Daura Farouk Umar Farouk a duk wani lamari wanda ya shafi Hausa ko Hausawa a duk inda suke. “Ina jin dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar musamman a tsakanin masarautun ta sa Sarkin Karma da ke Yamai a Jamhuriyyar Nijar ya nada ni Sarkin Yakin Matasan Hausawan Afirka, an kuma yi bikin nadin a ranar 9 ga  Mayun bara a birnin Yamai.

Kabilun Yarbawa da Ibo da Tibi babu wanda bai nada Ibrahim Sambo a sarauta ba. Misali, sarautar “Tsau” da kabilar Tibi suka ba shi wanda aka yi masa nadin a Arewa House da ke Kaduna a shekarar 2017, sai kuma ta “Agunechemba I” daga kabilar Ibo ita ma a  2017 sai kuma ta “Atunluse of Ilebaland” wato Zaki Mai kariya ga kasar Ileba. Sai kuma sarautar “Alaanu Mekunu Agbaiye” wato ‘Mai tausayin Talakawan Duniya’ wadda matan kabilar Yarbawa mazauna Amurka suka ba shi wadda kuma za a yi masa nadinta a gobe Asabar din.

Ba a masarautu kawai Maga-isan Katsina ya samu mukamai ba, yana daya daga cikin mutane uku na Duniya da suka samu nadin girmamawa na Kwame Nkurma ta “PAN AFRICA LEADERSHIP”. Sauran biyun da suka samu irin wannan karramawa sun haɗa da Julius Nyerere tsohon shugaban Kasar Tanzaniya da kuma tsohon shugaban Kasar Afirka ta Kudu marigayi Nelson Mandela. An ba Ibrahim Sambo Magnet digirin Dokta daga, Jami’ar ‘European – American a ranar 3 ga watan Yuni ta shekarar 2017.

Dokta Magnet ya ce, shi a rayuwarsa babu abin da yasa a gaba illa ganin al’umma suna zaune lafiya da juna a ko’ina suke a duniya domin dai dukkanmu Allah ne ya halicce mu daga Annabi Adamu da Hauwa. Har ma sai ya kawo wani misali,”A lokacin da ake neman gudunmawar jini ga maras lafiyar da ke bukata, ba batun addini ko yanki ko kabilar da mai bayar da gudunmawa ake kallo ba, abin da zali yi don ceton rai saboda an san dai mutum ne wanda asalinsa Hauwa da Adamu”. Akan haka ne, ya yi kira ga al’umma da kowa ne lokaci su zamo masu kaunar juna ne da kuma kyakkyawar alaka. “Tashin hankali ko nuna kabilanci ko bambanci akida ko siyasa da sauransu ba bu inda zai kawo wa kowace irin kasa ci gaba”, kamar yadda Mai tausayin Talakawan Duniya, Maga-isan Katsina Dokta Ibrahim Sambo Magnet ya ce.