Da Dumi Dumi

Gobe za a gwabza wasa tsakanin Real Madrid da Sebilla, jibi kuma Liberpool da Man United

A ci gaba da fafatawa a Gasar La-Liga ta Spain mako na 20 a gobe Asabar ake sa ran za a gwabza wasa a tsakanin kulob din Real Madrid da na Sebilla.

Wasan zai gudana ne a filin wasa na Madrid da misalin karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.

Madrid ce ta biyu a kungiyoyin da ke fafatawa a gasar yayin da Sebilla kuma take matsayi na hudu.

A gasar Firimiya ta Ingila kuwa, a jibi Lahadi ce za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Liberpool da na Manchester United.  Wannan shi ne wasa karo na 23, koda yake Liberpool tana da kwantan wasa daya da kulob din West Ham United.

Kawo yanzu Liberpool ce take saman teburin gasar da maki 61 a wasanni 21 yayin da Manchester United take da maki 34 a wasanni 22.

ADVERTISEMENT
Share