Da Dumi Dumi

Gudunmuwa ga Gwamna Masari

Da farko ina yi wa sabon gwamna Aminu Bello Masari murna da maraba da shiga gidan Gwamna, wani buri da ya dade a zuciyarsa. Kowa ya san an sa wa jihar Katsina ido, jihar Shugaban kasa. Fatana kar sabon Gwamna ya zama kamar sabon angon da ke wa amarya alkawari ba tare da damuwa da ita ba don ya tare.

A tashin farko yana da kyau gwamna ya bayyana dukiyar da ya mallaka, kamar yadda Baba Buhari ya yi. Haka ya umarci duk mataimakansa kamar ‘yan majalisa, mashawarta da kwamishinoni su bi sahu. Hakan zai ba su kima a idon mahasadda. Ya san wadanda zai ba kwamishinoni da Mashawarta, ya tantancewa wajen tabbatar masu da kujerunsu, domin alkawalin nan na canji.
Ya zama wajibi Gwamna Masari ya wadata jihar da ruwan sha, saboda wasu dalilai, farawa da cewa yana da ilimi kan wannan harka, sannan ana matukar bukatar ruwa a sassa da daman a jihar, musamman a irinsu Mashi da Muduru da Makurda da sauransu. Domin a jihar Katsina a inda dabobbi suke shan ruwa nan mutane suke sha, a babban birnin kuwa jarkoki sun fi mutane yawa, domin ko kai kanka Gwamna a da jarkokin gidanka sun fi yawan ‘ya’yanka da matanka, amma komai ya sauya ma!
Sannan muna sane da yadda ya rika yin kamfen na zai inganta ilimi a jihar, inda har angon ke cewa ‘ya’yansa da na mukarabansa za su koma makarantun Gwamnati. Tabbas akwai jan aiki wajen dawo da darajar ilimi a Katsina, jihar da ta yi suna wajen ilimi a baya. Ba malamai a makarantu, sannan ba kayan aiki, wasu makarantun ma idan ana ruwan sama sai dai a tada daliban don ba rufi, wasu ko a gindin bishiya ake karatun, kuma ka iske wani lokaci ko alli babu, yayin da ake gargadin malamai da su rika tattalin alli, duk da cewa gwamnatin da ta shude ta gyara makarantun kan hanya, kuma tana gorin biyan kudin jarrabawar fita daga sakandare, inda har cewa suke sun biya kyauta, amma shin ana cin jarrabawar? Duk da haka ya ci gaba da ba da sukolashif ga hazikai a nan cikin gida da kasashen ketare.
Tabbas an bar kiwon lafiya a wani sumammen yanayi, inda asibitoci bakin hanya da na babban birnin kadai aka zamanantar, sai wasu daidaiku aka yi wa kwalliya, an bar kauyuka da rakwababbun kangwaye da sunan asibitoci. Bayan ko Kansila ba zai taba kai ‘ya’yansa ba, balle mace da juna biyu.
Muna bukatar daidaito tsakanin dan PDP da APC, kar a nuna bambanci, domin Shugaba na kowa ne. Kuma ko ‘yan PDP ai ‘yan uwan Gwamnan ne! Domin idan aka yi wasa aka wa wasu ba a yi adalci ba, aka bi ta da kulli za a sha mamaki, inda ba sai an je ko’ina ba wadanda suke wa Gwamna maraba za su bi shi da ruwan duwatsu! Domin caimomin nan sun taka rawar gani wajen yi wa sabon Gwamna kara. Hasali ma mutane da dama sun ba da gudumawa ga wannan gwamnatin. A yi koyi da Buhari, a yi adalci tsakanin mutanen Daura, Katsina da Karaduwa.
Wajen bunkasa noma da kiwo, a fara gano su wane ne manoma, kuma su za a bai wa taki, ba mukarabai ba a sunan siyasa. Wannan ne abin da mutanen karkara za su mora. Domin a kauyuka da dama a jihar nan babu makarantun Islamiyya, balle na boko ko asibitoci. Haka maula da barace-barace sun yawaita a jihar a bisa haka gara ya ci gaba da tsohon tsarin ciyar da almajirai ko ya hana bara baki daya.
Ya kamata a tura malaman addinin karkara domin a wasu kauyukan ko alwala ba a iya ba. Haka a gina tituna tsakanin kauyuka da birane, da tsakanin kauyuka da kauyuka. Kuma a gabatar da auren zawarawa da zaburar da samari da ‘yan mata ganin yadda harkokin daudu, madigo da zina suka yawaita a jihar, musamman a makarantun sakandare. Sannan a tura tawagar masu wa’azi don Musuluntar da Maguzawa.
A kafa Katsota watau hukumar da zat a bi lungunan jihar nan tana
tabbatar da ana tsaftace muhalli, tana bude hanyoyi tsakanin gidaje da shagunan kan hanya. A gayyato masu hannu da shuni ‘yan asalin jihar su zuba jari don gayyata. Kuma wajen daukar sababbin ma’aikata kamar yadda sabon Gwamna ya yi alkawari ya kamata a cika ta hanyar bude kamfanoni da za su dauke matasa daga majalisun bin inuwa, musamman masana’antun da ke da alaka da noma. Kuma a ba wasu jarin bude gidajen kaji da kiwon kifi domin wadannan hanyoyi na amun alheri fiye da aikin gwamnati wanda zai barka da bashi.
A dauki matasa ayyukan yi, musamman ya dauki kurata ta yadda jihar Katsina za ta hau hanyar kafa ‘yan sandan talakawa. Kuma a tallafa wa kungiyoyi da kulub-kulub.
A wannan lokacin idan da gaske ana son bunkasa ilimi a jihar Katsina ya zama wajibi a tafi da marubuta, a hanyar yin gasa daukar nauyin kungiyoyin marubuta. Domin marubutan jihar Katsina sun zama ‘yan kallo, sai dai su rika sha’awar marubutan makwabtan jihohi.
Daga karshe ina son kowa ya fahimci cewa wannan gwamnatin talakawa ce, mu muka zabo ta don ta nuna bambanci, kuma ina da kyakkyawan fatan cewa Shugaba Buhari ba zai sa ido abubuwa su sukurkurce a jiharsa ba. Allah ya raya jihar Katsina.
Buhari Daure +2347035986444 Muryar Talaka kofar kaura, Katsina

Share