✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwagwarmayar rayuwa: Waiwaye adon tafiya (3)

Daidai da rana ɗaya Mai girma Gwamna bai taɓa ce mini ka rubuta kaza ka kare ni ko gwamnati ba. Duk abin da nake rubutawa…

Daidai da rana ɗaya Mai girma Gwamna bai taɓa ce mini ka rubuta kaza ka kare ni ko gwamnati ba. Duk abin da nake rubutawa gabana ake yi ko kuma in je ma’aikatar da abin ya shafa in samo bayanin da ya dace in fitar da shi ga jama’a.

A lokacin da na fara samunsa da ƙorafe-ƙorafen da muke samu ta Soshiyal Midiya, sai ya ce “AbdulHadi ka riƙa zuwa ma’’aikata ko cibiyar da abin ya shafa, ka ce na ce a bincika kuma a yi abin da ya kamata. Ko mi ke nan sai ka zo ka yi mini bayani.”

Tun daga ranar na samu wannan dama ta kai koke da shawarwarin al’umma zuwa wuraren da suka kamata. Babu ɓangaren da ba mu taɓa ba; albashi, karin girma, tallafin karatu, fansho, ayyukan gona, lantarki, lafiya, ilimi (musamman gyaran makarantu) da sauransu.

Zuwa yanzu, za a fahimci cewa aiki ya kankama, alhamdu lillah!

A cikin hulɗa ta aiki na yau da kullum, akwai abubuwa da dama da suka faru, waɗanda suka ƙara fito da nagarta da kyakkyawar hulɗa da sauƙin kan Gwamna Aminu Masari.

Akwai lokacin da wani ya yaɗa labarin ƙarya cewa wai gwamnati ta sayi makarar ƙarfe tana rarrabawa a masallatai. Da na yi wa Gwamna bayani sai na ce masa zan mai da martani. Sai ya ce “AbdulHadi, me za ka rubuta, ka ce ba mu saya ba? Ai da ma mutane sun san ba mu saya ba, wanda kuma ya yi mana ƙarya shi da Allah.” Sai da na sake ɗaukar lokaci ina yi masa bayanin nisan inda labarin ya kai, sannan ya ce “To rubuta, ka ce ba mu saya ba, amma ka sani ba mu da haƙƙi da wadansu mutane da suka wuce al’ummarmu ta Jihar Katsina.”

A cikin tsare-tsaren daidaitawa da sa ma’aikatan ƙananan hukumomi inda suka dace, sai wadansu suka juya abin cewa za a kori ma’aikata ne da wayo. Wannan ma da muka tattauna sai ya ce, “Je ka ƙaryata amma ni a wurina ba wani abu ba ne saboda ba mu korar ba, kuma idan muka kora za a gani.”

Akwai lokacin da aka yi mini rasuwa na tafi Faskari, sai aka yi mini waya, aka ce yana nemana. Nan da nan na kama hanyar Katsina, ina isa na same shi a ofis, yana ɗaga kai ya kalle ni sai ya ce “Har ka dawo Faskarin? Sai na kada baki na ce, Baba cewa aka yi kana nemana. Nan take fuskarsa ta canja, ta cika da alamun damuwa. Sai ya ce “Cewa na yi a nemo ka a waya saboda abin da nake son ka yi ya shafi Funtuwa da Mahuta ne, da sai ka biyo ta can idan za ka dawo.” Na ce ai ba komai.

Unguwar Ka-Sha, wani ƙauye ne da ke kan hanyar Marabar kankara zuwa danja. Wata rana muna kan hanyar za mu je Abuja sai muka tsaya Sallah a masallacinsu (ƙa’ida ce ta Dallatu, idan muna tafiya duk sa’ar da lokacin Sallah ya yi zai ce a tsaya a yi). Allah cikin ikonSa kafin in shiga masallacin na kalli makarantarsu, na kuma ga halin da take ciki. Da na same shi a cikin masallacin sai nake gaya masa abin da na gani. Nan take ya ce idan mun gama Sallah yana son ya duba ta kafin mu wuce. Muna gamawa kuwa ya duba ta kuma ya tattauna da al’ummar tare da shan alwashin gyaran makarantar. A yanzu maganar da nake, matsalar wannan makaranta ta kau, domin bayan gyara har ajujuwa aka kara musu, aka kuma gina musu kewaye guda takwas.

‘Protocol’ akan fassara shi da tsarin da ake yin abu; to akwai ranar da yana yi mini wani bayani sai na yi gajen haƙuri, gami da ƙarancin sanin ‘Protocol.’ Sai kawai na ce cikin Inglishi, ‘Yi hakuri yallabai, na katse maka magana…’ sai na ci gaba da bayani, shi kuma sai ya tsai da nasa jawabin ya koma saurarena har na gama. Bai nuna damuwa ba kuma maganar ke nan har yau saboda ya fahimci koyo muke.

Za mu kammala makon gobe