✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna na ADP a Jihar Oyo

A ranar Lahadin da ta gabata ce Allah Ya yi wa shahararren ɗan wasan barkwanci nan na Kudancin Najeriya, Moses Olaiya Adejumo, wanda aka fi…

A ranar Lahadin da ta gabata ce Allah Ya yi wa shahararren ɗan wasan barkwanci nan na Kudancin Najeriya, Moses Olaiya Adejumo, wanda aka fi sani da Baba Sala rasuwa, bayan ya daɗe yana jinya, sakamakon tsufa, kamar yadda mai taimaka masa na musanmman a kafafen sadarwa, Isaac Hastrup ya bayyana.

Marigayin, wanda ya rasu a gidansa da ke garin Ilesa a Jihar Osun, an kai gawarsa ɗakin ajiyar gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo na garin Ilesa. Kuma ya rasu ne yana da shekara 83 a duniya.

A sakon ta’aziyyar da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya fitar, ya bayyana rasuwar Baba Sala a matsayin babban rashi ga duniyar wasan kwaikwayo da kasar nan baki daya. Ya ce Nijeriya ta yi rashin dan wasan kwaikwayo haziki mai hikima.

A sakon Obasanjo ya ce “A yayin da muke godiya ga Madaukakin Sarki Allah da ya ba shi tsawon kwana, sai dai muna dada jajanta wa iyalinsa, ganin irin girman rashin shugaban da aka yi. Rashinsa ba ga iyalinsa ba ne kadai, rashi ne ga dukan ’yan Najeriya. Don haka ina mika gaisuwar ta’aziyya ga dukan al’ummar Najeriya saboda wannan babban rashi da muka yi.”

A sakon ta’aziyyar Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola ya bayyana rasuwar marigayi Olaiya da babban rashi. Lokacin da yake mika wa iyalinsa sakon nasa, Gwamnan ya ce: “Rasuwar Pa Moses Olaiya Adejunmo, wanda wasanninsa na barkwanci suka shahara, ta kawo karshen ingantaccen wasan kwaikwayo da barkwanci a kasar nan.”

A takardar da Kakakin Gwamnan, Sola Fasure ya sanya wa hannu, ya ce rasuwar Baba Sala ta samar da babban gibi a duniyar wasan kwaikwayo, wanda zai yi wahala a samu mai cike shi.