✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Legas ya karbi bakuncin wasu fitattun ‘yan kwallon duniya

A ci gaba da shiryen-shiryen wasan kwallon kafa na musanmman da gwamnatin jihar Legas ta shirya a wani bangare na yin bankwana da gwamnan jihar…

A ci gaba da shiryen-shiryen wasan kwallon kafa na musanmman da gwamnatin jihar Legas ta shirya a wani bangare na yin bankwana da gwamnan jihar Akinwumi Ambode wanda zai ajiye ragamar mulkin jihar nan da kwanaki 12 masu zuwa, manyan fitattun ‘yan kwalon duniya ‘yan asalin kasashen Afirka sun ziyarci gwamnan a fadar gwamnatin jihar da ke babban birnin jihar wato Ikeja a yankin Alausa.

Zakarun ‘yan kwalon da suka ziyarci gwamnan sun hadar da Kanu Nwankwo da  Finidi George sai  Victor Ikpeba tare da  El Hadji Diouf da Diomansy Kamara sai  Didier Zokora da  Khalilou Fadiga Austin Eguavoen da Mutiu Adepoju sai Waidi Akanni tare da Uche Okechuku da  Seydou Keita, a lokacin da yake karvan bakun cin manyan ‘yan wasan kwallon kafar Gwamnan Ambode ya bayyana harkar wasan kwallon qafa a matsayin wata kafa ta bunkasa tattalin arzikin kasa tare da kulla zumunta da tabbatar da zaman lafiya, “Tun farkon lokacin da na zama gwamana na yi nazarin yadda zan bukasa tattalin arzikin jihar Legas ta fuskar wasannin da fannin bude ido, kwallon qafa bangare ne da idan kasashen mu na Africa suka rike shi da mahinmmanci za a sami bunkasar tattalin arzikin  yankin tare da daukaka zumunta a tsakanin kasashen, domin ‘yan kwallon wannan nahiya sun yi fice ta yadda ake damawa dasu a duk wani kulub mai tashe a duniya” in ji gwamnan Ambode.