Gwamnan Oyo ya nada shugabannin riko na kananan hukumomi

Takaddama a tsakanin Gwamnan Jihar Oyo, Mista Seyi Makinde da tsofaffin shugabannin Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Jihar (ALGON) ta kawo karshe a ranar Litinin da ta gabata bayan da Gwamnan ya rantsar da sababbin shugabannin riko na kananan hukumomi 33 da hukumomin raya kasa (LCDA) 35.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Mista Adebo Ogundoyin ne ya jagoranci zaman tantance sunayen sababbin shugabannin 68 da Gwamnan ya rantsar.

Gwamna Makinde ya rantsar da sababbin shugabannin rikon ne a daidai lokacin da tsofaffin zababbun shugabannin da ya  sauke suke ci gaba da fafutikar komawa ofisoshinsu, bisa hujjar cewa an kore su ne ta haramtacciyar hanya domin wa’adin aikinsu bai kare ba. A makon jiya ne Shugaban Kungiyar ALGON, Yarima Abass Aleshinloye ya umarci dukkan tsofaffin zababbun shugabannin 68 su koma ofisoshinsu domin kama aiki kamar yadda tsarin mulki ya tanada cewa irin wadannan zababbun shugabanni wajibi ne su cika wa’adin shekara 3 a ofis wanda suke ikirarin cewa ba su kai ga cika wa’adinsu ba aka kore su.

Jim kadan da bayar da wannan sanarwa ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu ya ja kunnen Kungiyar ALGON kan ta yi taka-tsantsan don kauce wa abin da zai iya haifar da hargitsi a tsakanin jama’a.

Kwamishinan ya shawarci kungiyar ta dauki matakin da ya kamata musamman zuwa kotu domin warware matsalarta maimakon irin wannan mataki da zai iya tayar da zaune-tsaye.

ADVERTISEMENT

A ranar Larabar makon jiya ne, Yarima Abass Aleshinloye ya yi kokarin shiga ofishinsa a Sakatariyar Karamar Hukumar Oluyole da ke garin Idi-Ayunre domin fara aiki kamar yadda ya umarci sauran shugabanni su yi. Sai dai jami’an tsaro ba su kyale shi ya shiga cikin ofishin ba in ji wata majiya da ta tabbatar da cewa babu wani tsohon shugaban karamar hukuma da ya yi aiki da umarnin kungiyar ta ALGON.

 

Share