✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta umarci DSS da a saki Dasuki da Sowore

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya DSS  da ta saki tsohon mai ba da shawara kan tsaro na kasar, Kanal Sambo…

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya DSS  da ta saki tsohon mai ba da shawara kan tsaro na kasar, Kanal Sambo Dasuki da Omoyele Sowore mai jaridar Sahara reporters.

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ne ya bayar da sanarwar a ranar Talata.

Ministan ya ce, gwamnati ta amince da sakin mutanen biyu ne domin mutunta hukuncin kotuna daban-daban na neman belin da suka yi.