✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta sake mika wa majalisa bukatar kirkirar sabbin masarautu

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da bukatar kirkirar sabbin masarautu a jihar na shekara 2019, inda ta bukaci karin masarautu guda hudu  a…

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da bukatar kirkirar sabbin masarautu a jihar na shekara 2019, inda ta bukaci karin masarautu guda hudu  a fadin jihar, wadanda suka hada da Rano da Gaya da Bichi da kuma Karaye.

Bayanin hakan na kunshe acikin wata takarda da Kwamishinan Watsa Labarai a Jihar Kwamared Muhammad Garba ya sanya wa hannu.

Takardar ta bayyana cewa tuni aka mika kudurin dokar ga Majalisar Dokokin Jihar Kano don daukar matakin da ya dace.

Takardar ta kara da cewa wasu daga cikin masarautun sun yi mulki shekaru da dama, sai dai lokacin Jamhuriyya ta biyu an yi kokarin farfado da su wanda ba a kai ga cin nasara ba,

An jaddada cewa an tattauna batun na kudurin dokar masarautun sosai a taron Majalisar Zartarwar domin ganin cewa masarautun za su taimaka wajen kawo ci gaba ga al’uumar jihar.

Takardar ta kara da cewa an gudanar da gyara kan dokar masarautun ta shekarar 2019 bisa bukatar ghakan daga al’ummar jihar bayan soke hukuncin da Babbar Kotun Jihar ta yi bisa hujjar cewa korafin da aka gabatar ga majalisar wani ne ya yi wanda ba mamba ba ne a majalisar.

A cewar takardar Majalisar Zartarwar ta bukaci Majalisar Dokokin da ta yi gaggawan tabatar da dokar saboda amfanin al’ummar Jihar Kano.

Abin da masana suke fada

Dokta Tijjani Naniya malami ne a Sashen Tarihi a Jami’ar Bayero ya bayyna cewa kirkirar masaurautun da gwamnatin Jihar Kano ta yi ba ya bisa ka’ida, a cewarsa abu ne da zai kawo wargajewar masarautu a maimako ci gban Jihar.

A cewarsa kafa masarautu ba abu ne na ra’ayi ba, tarihi ne yake kawo kafa masarautu. “Idan muka dauka ko ita Kano kafin kafuwarta a da jama’a a warwatse suke a yankuna daban-daban, misali akwai jama’an Dutsen Dala da na Goron Dutse da na Fanisau da sauransu, lokacin da Barbushe ya buwaya ya rinjayi sauran don haka sai aka kafa masarauta a karkashinsa. Daga baya kuma da Bagauda ya zo ya da yaki Kano sai ya kafa sarauta ta sarki. Lokacin da Kanon ta bunkasa ita ma sai ta je ta kama wasu garuruwa da ke gefenta kamar su Rano da Karaye da sauransu ta dawo da su karkashinta. Haka kuma da aka yi jihadi masu jihadi suma suka yi nasarar sai suka kafa nasu mukin. Da Turawa suka zo ba su taba tsarin mulkin sarautar gargajiya ba. Da aka bayar da mulkin kai aka yi larduna suma ba su taba tsarin mulkin gargajiya ba. Haka kuma da aka yi jihohi, ba a taba sarautu ba sanin cewa wuraren suna da tarihinsu. Kin ga ashe kafa masarautu ba abu ne na son zuciya ba.”

Dokta Naniya ya bayyana cewa a baya ma a Jamhuriyya ta biyu Gwamnan Kano Abubakar Rimi ya yi kokarin kirkirar wasu masarautun sai dai abin bai yi nasara ba kasancewar an yi shi ba bisa ka’ida ba.

“Idan za mu iya tunawa Shugaban kasa marigayi Sani Abacha ya samu matsala da Sarkin Kano Ado Bayero, amma bai yi yunkurin hukunta shi ta hanyar kirkirar wasu masarautu a Kano ba. Shi ya sa muke kira ga gwamnati cewa idan tana da matsala da masarauta ta dauki wata hanyar ta warware ta, amma ba ta hanyar kaccacala tarihi ba.”

A cewarsa gudummowar da sarakuna suka bayar tana da yawa wajen kafa masarauta, wanda bunkasarsu ce ma ta janyo aka samu Jihar Kanon, “Kafa masarauta abu ne na tarihi, aiki ne wadansu suka dau lokaci suna yi inda suka yi amfani da karfinsu da iliminsu wajen kafa shi shekara dubu aka yi ana kafa wanann tarihin. Ita kanta jihar ma ta samu ne saboda darajar masarautar, sai kuma a zo a wulakanta ta?. Idan muka yi haka mun raina mafarinmu ke nan. Idan aka ci gaba da haka watarana za mu rasa tarihinmu kamar yadda muka rasa na badala.”

Barista Dalhatu Usman ya bayyana cewa sake dokar kirkirar masarautun da gwamnatin ta yi abu ne da yake bisa ka’ida, domin tsarin shari’a ya bayar da dama a yi doka yau gobe a sake yin wata. “Idan kin dauki kundin tsarin mukin kasa za ki ga ana cewa wanda ka yi wa gayra, don haka za ka iya yin doka yau gobe ka gyara.  Idan kika dauki kundin laifuffuka shi ma an yi masa gyara kuma ba wai an gama ba ko gobe za a iya kara gyara shi. Wannan ba laifi ba ne.”

A cewar barista kotu ba ta hana Gwamnatin Kano ko Majalisar Dokoki ta yi wata sabuwar dokar ba illa ta nuna ba ta gamsu da hanyoyin da aka bi wajen yin dokar ba.