✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya ci mutum 21 dabbobi 80 a Bauchi

A ranar Asabar da ta gabata ce wani hadarin mota a kan hanyar Bauchi zuwa Maiduguri ya hallaka akalla mutum 21, sannan dabbobi 80 suka…

A ranar Asabar da ta gabata ce wani hadarin mota a kan hanyar Bauchi zuwa Maiduguri ya hallaka akalla mutum 21, sannan dabbobi 80 suka kone kurmus.

Tsohon Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Bauchi Alhaji Umar Ibrahim Sae ne ya sanar da haka lokacin da yake fayyace wa wakilinmu yaddda lamarin ya faru.

Ya ce binciken da suka yi bayan lamarin ya faru shi ne mutum shida daga cikin wadanda hadarin ya rusta da su daga Sade suke, sannan mutum biyar daga Lanzai duka  a Karamar Hukumar Darazo da ke Jihar Bauchi.

Ya ce mutanen sun fita ci -ani ne, suka dawo don yin Babbar Sallah sai wannan tsautsayi ya fada musu kilomita daya kafin su isa garin Sade.

Sai ya zargi Hukumar Kula da Manyan Hanyoyi ta Tarayya (FERMA) cewa ita ke da alhakin wannan hadari saboda ita ce ta tona rami da zimmar za ta cike, amma aka yi wata biyu ba ta cike ba.

Wani mutumin Sade da ya ga yadda lamarin ya auku ya ce FERMA ta tona rami za ta yi gyara a kan kwalta. Wannan rami ne wata mota ta daka da karfi sai tayar motar ta fashe lamarin da ya kai ga motoci uku suka kara da motar kuma take ta kone da mutane da dabbobin da ke cikin motocin.

Shugaban Riko na Karamar Hukumar Darazo, Alhaji Gara’u Adamu ya ce hadarin ya hada da matafiya da suka taso daga Bauchi da Abuja da Sade zuwa Kari, da kuma wadansu da suka taso daga Lanzai, inda hadarin ya rutsa da su a daidai kauyen Kari zuwa Sade kimanin nisan kilomita daya.

Shugaban ya ce, “Mutum 21 ne Allah Ya amshi ransu a lokaci guda sakamakon hadarin. Bayan mutanen da suka rasu, akwai dabbobi 80 da suka kone kurmus a hadarin, An yi rami guda aka zuba gawarwakin dabbobin.”

Ya ce an kai wadansu daga cikin mutanen da hadari ya shafa zuwa Asibitin Darazo wadansu an wuce da su Bauchi domin yi musu jinya.

Sai ya mika ta’aziyya ga al’ummar karamar hukumar da na jihar da kasa baki daya bisa wannan hadari.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da aukuwar hadarin ya ce wadansu sun gano sunayen ’yan uwansu ne ta hanyar takardun da suka cike a tashar mota.