✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (8)

Abubuwa uku za su sa a ki amincewa da haka. Na farko dai garin na Daura dakaru, jarumai, maharba ne suka samar da shi, bai…

Abubuwa uku za su sa a ki amincewa da haka. Na farko dai garin na Daura dakaru, jarumai, maharba ne suka samar da shi, bai yiwuwa a ce macijiya ta hana dibar ruwa a rijiyar da ke da muhimmmanci ga rayuwar al’ummar. Na biyu, an yi nuni da cewa ita kanta Saurauniyar sunanta Fatima, kila Musulmi ne ke nan, da wuya kuwa Musulmin kwarai su amince da tsibbu ko tsafi irin wannan. Abu na uku, shi kansa tadi irin na macijiya abu ne da ya dade cikin tarihi da labaran wannan yanki, amma an fi dora shi bisa bauta irin ta gumaka ko arnanci, ba dai Musulunci ba. Ke nan al’ummar Daurar arna ne, ko masu bautar gumaka in har suna bautar maciji ko macijiya.
Idan ma dukkan wadannan bayanai ba su gamsar ba, to za mu iya amincewa da cewa labarin macijiyar shi ma kamar na Bayajidda, mai kama da ta-zo-mu-ji-ta-ne, domin kuwa kamar yadda aka gani a kasar Yarbawa yadda aka ce Bayajidda ya samar da kasashen Hausa Bakwai da Banza Bakwai, haka shi ma Oduduwa ya haifi ’ya’ya da suka samar da kasashen daular Yarbawa. To haka kuma an ga irin wannan labari na maciji ko macijiya da masana suka kawo game da wannan yanki na Yammacin Sudan, ba Daura kurum ba, mai nuna alamun cewa duk kamar shaci-fadi ne. An ga irinsa a Daular Songai, inda aka nuna cewa wanda ya samar da daular, wato Za Alayaman, sai da ya kashe maciji ko macijiya kafin ya hau gadon sarauta. Haka kuma bincike ya nuna cewa an samu irin wannan labari na maciji ko macijiya a tarihin ginuwar daulolin kasar Yarbawa da Dahomey. Ba ma a wannann yanki kawai ba, hatta a yankin Turawa da Larabawa an ga irin wannan yanayi na kashe maciji ko macijiya domin a hau karagar mulki.
kila in har za mu amince da aukuwar wannan batu na macijiya a cikin rijiya, sai dai mu nuna cewa lallai al’ummar da iyalai ko dakarun Abu Yazid suka iske, masu bautar macizai ne, irin wadannan macizan ne na bauta suka kashe, shi ya sa suka samu damar mulkar al’ummar cikin ruwan sanyi, ba wai wata macijiya ba ce ta yi tsaye ta hana rayuwa gudana.
Saboda haka muna iya cewa da alama ba macijiya a cikin rijiyar Kusugu in har an yi rijiyar sai dai wani abu can daban. In ma har an yarda da an yi macijiyar a cikin rijiyar to abin bauta ce, ba wai mazauniyar rijiyar da hana dibar ruwan ba. Amma kamar yadda wasu masana ke nuni, tana yiwuwa ba ma macijiya ba ce, wani dakare ne ke zaune a rijiyar saboda muhimmancinta ga rayuwar al’ummar, kuma shi ne ke hana a dibi ruwa a rijiyar sai ranar Juma’a kawai, ba don komai ba, sai ganin in ya bar mutane su rika dibar ruwan rijiyar kowace rana, ana iya samun wani lokaci da rijiyar za ta kafe, a rasa ruwa, saboda yanayin wajen da rijiyar ke zaune.
Wannan na iya zama da kanshin gaskiya in aka yi la’akari da tunanin wasu masana da ke nuna cewa a da birnin Daura na yanzu ba inda yake zaune yake ba, akwai tsohon birnin, inda can jama’a ke zaune, kuma rashin ruwan ya shafi falalen yankin tsohon birnin har zuwa yankin sabon birnin Daura na yanzu. Kamar yadda irin wadannan masana suka yi nuni, an ce wani Bafullatani ne da dabbobinsa ya gano inda rijiyar Kusugu take yanzu daga daya daga cikin dabbobinsa da ba ta shan ruwa, duk lokacin da suka je inda ake ba su ruwa, saboda rashin ruwan, sai da makiyayin nan ya bi wannan dabba, ya ga a cikin wata sarkakiya take labewa tana shan ruwa da ke bulbulowa, daga nan ne, ya fahimci cewa ashe akwai idon ruwa a wurin, wannan idon ruwan shi ne mabubbugar rijiyar ta Kusugu, kuma shi ne musabbabin tasowar mutane daga tsohon birni zuwa sabon birni, kamar yadda binciken ya nuna.
Idan har wannan bincike zai iya samun karbuwa za a iya cewa ke nan, kila ba macijiya ba ce zaune a cikin rijiyar, kila wannan da ya gano mabubbugar ruwan shi ne mai gadin abinsa, kila ma kudi ya sa ana biya domin samun ruwan sha. Wannan al’ada kamar yadda masana suka nuna dadaddiyar al’ada ce a inda duk ruwa ke da matsala. Daga nazarin sassan hamadar Sahara da yankin kasashen Larabawa za a ga gudanuwar irin wannan al’ada. Ko a zamanin Manzon Rahma (SAW) a Madina, yawancin rijiyoyin birnin Madina hannun Yahudawa suke, su ne masu kula da su, duk mai bidar ruwan sha, sai ya biya da dabino ko makamancin haka, sa’annan a ba da dama a debi guga daya ko makamancin haka. Idan kuwa wannan al’adar ta zaunu, ba abin mamaki ba ne a ce an ga irin ta a birnin Daura a wancan lokaci, a maimakon zaman macijiya a cikin rijiya ta hana dakarai dibar ruwa.
kila abin da wani zai iya tambaya shi ne, to, in ba a kashe macijiya ba, to wa ko me Bayajidda ko wani daga cikin iyali ko dakarun Abu Yazid ya kashe har ya sa ya auri Kuyanga da Sarauniya har daga baya ya zama Sarki? A halin yanzu ba mai iya tabbatar da abin da ya faru, domin akwai masana masu hasashen cewa tun da ba macijiya, ba yadda za a kashe macijiya, ke nan ba auren Kuyanga ko Sarauniya Daurama. Wasu kuma na nuni da cewa ai tun da yake tun da farko ba Bayajidda ko Abu Yazid, ke nan ba batun zuwa Daurar balle a kashe macijiya har a yi aure a samar da ’ya’ya da suka kasance asalin Hausa Bakwai da Banza Bakwai. Wasu kuma sun yi nuni da cewa idan kuwa ba auren Daurama da wani wai shi Bayajidda ko Abu Yazid, ke nan ba Karba-Gari ko Bawo, idan ba su kuwa ke nan ba ’ya’yansu da suka samar da kasashen Hausa Bakwai ko Banza Bakwai.  
Za mu ci gaba